Rijiya

    5.2 5 Rijiya

    Wannan ma wasa ne na yara maza. Abubuwan da ake buƙata kafin gudanar da wannan wasa sun haɗa da yashi da kuma riguna. Akan gudanar da wannan wasa da hantsi ko da rana ko kuma da dare, musamman idan akwai farin wata. Wasan ba ya tafiya da waƙa.

    5.25.1 Yada Ake Wasa

    Yara za su tona rami kan yashi da aka zube domin gini. Ramin zai kasance mai ɗan faɗi, daidai da yawan yara. Bayan rami ya kammala, kowane yaro zai sanya ƙafafunsa ciki. Sannan za a mai da ƙasa a bisne ƙafafun. Zai kasance kusan guiwar yaran zuwa ƙasa duk sun lume cikin ramin.

    Bayan komai ya kammala. Za a ƙidaya daga ɗaya zuwa uku. Wannan na nuna an ba da dama kowa ya zare ƙafarsa daga cikin ramin. Saboda haka, kowa zai fara ƙoƙarin zarewa cikin dabaru da hikimomi iri-iri. Duk wanda ya samu ya zare ƙafafunsa, zai yi sauri ya nannaɗa rigarsa, sannan ya shiga bugun duk wanda ƙafarsa ke cikin ramin. Waɗanda ba su samu dammar cire ƙafafunsu da wuri ba, za su sha bugu ƙwarai da gaske.

    5.25.2 Tsokaci

    Wannan wasa na samar da nishaɗi ga yara. Sannan yana koya musu jarumta da juriya tare da ƙoƙari. Dole ne yaro ya yi ƙoƙarin fitar da ƙafafunsa da wuri gudun shan bugu. Sannan yaran da suka yi rashin sa’a ba su fita da wuri ba, dole ne su je ruirin dukan da za su sha. A cikin ana dukan nasu kuma suke ci gaba da fafutukar fitar da ƙafafun nasu, har sai sun samu nasara. Lallai wannan bajinta ce.

    WASANNI A ƘASAR HAUSA

    Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.