Ticker

    Loading......

5.2 Rawa

 

Citation: Bunguɗu, U.H. (2021). Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar HausaAhmadu Bello University Press Limited.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar Hausa

5.2 Rawa

Rawa wata siga ce da waƙoƙin bara suka keɓanta da ita. Almajirai da sauran mabarata suna haɗa waƙoƙin da suke rerawa a lokacin da suke bara tare da rawa. Ga Almajirai rawar sosai ake takawa ta idan ana rera waƙar bara, domin sau da yawa rawar ce ke burge mata har su ba Almajiri sadaka ko da can da farko ba ƙuduri yin haka ba. Su mabarata waɗanda suke manya suna haɗa waƙoƙin da suke rerawa da rawa idan waƙar ba rubutatta ba ce. Ga ma abin da ake faɗa a cikin waƙar “Daudun Bara”:

 Jagora: Ni daudun bara ɗan galadima bara.

 Amshi: To.

 Jagora: Na saba bara bani kwana ban ciba.

 Amshi: To.

 Jagora: Kun ga rawar tuwo kun ga tattakin miya.

 Amshi: To.

 (Daudun Bara)

A ɗa na uku na wannan waƙa an nuna ana dafsa rawa sosai yayin da Almajiri ke rea waƙar. A waƙoƙin sauran mabarata ma na baka ana haɗa su da rawa a lokacin rera su. Misali waƙar “Madogara Annabi”

Madogara Annabi.

Annabi dai Annabi.

Babu kamar Annabi.

Madogara Annabi.

Way yi kamar Annabi.

Ku ba ni don Annabi.

Annabi jikan Nuhu.

 (Madogara Annabi)

Wannan waƙa mabarata manya ne suka fi amfani da ita, kamar guragu da kutare da makafi waɗanda ba su hardace wani abu daga rubutattun waƙoƙin wa’azi ko madahu ba. Ana rera wannan waƙa da ƙarfi sosai kamar dai mai rera ta ɗin ba ya cikin hankalinsa. Haka ma ana kaɗa kai da ƙarfi da wasu sassan jiki kamar kafaɗa a sadda ake rera ta. Waƙar mutum ɗaya ke rera ta, wato ba a cikin taro ba.


Post a Comment

0 Comments