Ticker

Babana Ya Saya Min kwallo

 5.24 Babana Ya Saya Min Ƙwallo

Wannan ma wasa ne na yara maza. An fi gudanar da shi lokacin damina, yayin da ƙasa ke da damshi. Yara masu ƙarancin shekaru ke yin sa, waɗanda ba su wuce shekaru shida zuwa ƙasa ba. Sannan babu wani wuri da aka keɓe domin wasan. Dangane da lokacin wasa kuwa, an fi gudanar da shi da hantsi ko da yamma. Ba a wasan da dare. Kayan aikin da ake buƙata domin wannan wasa shi ne ƙasa.

5.24.1 Yadda Ake Wasa

Akan yi amfani da ƙasa mai damshi yayin gudanar da wannan wasa. Yaro zai tara ƙasa ya mulmula ta wuri guda ta zama tamkar ƙwallo. Daga nan sai ya ɗauke ta a hannu, ya kuma ce:

“Babana ya saya mini ƙwallo ya ce kada na buga sai gobe da safe. Gobe da safe ta yi.”

Daga nan kuma zai jefa ƙasar sama kaɗan, sannan ya buga ta da ƙafa. Nan da dan za ta watse.

5.24.2 Tsokaci

Wannan wasa ne da ke samar da nishaɗi ga yara. Sanan yana nuni zuwa ga biyayyar yara ga iyayensu. Domin ga shi mai ƙwallo bai buga ba sai lokacin da babansa ya ba shi damar bugawa.

WASANNI A ƘASAR HAUSA

Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


Post a Comment

0 Comments