Mai Dawa

    5.28 Mai Dawa

    Wannan ma wasa ne na yara maza. Ana gudar da shi ne a dandanli, musamman lokacin farin wata. Kayan aiki da take buƙata shi ne ƙasa, da kuma batirin rediyo babba. Ba ya tafiya da waƙa, sannan yana cikin rukunin wasannin tsaye. 

    5.28.1 Yadda Ake Wasa

    Yayin da yara suka taru a wurin wasa, ɗaya daga cikinsu zai kasance mai dawa. Shi ne shugaban wasa. Mai dawa zai tara ƙasa mai ɗan yawa a gabansa. Sai kuma sauran yara su jeru a bayansa. Daga nan zai jefa babban batirin rediyo can nesa, iyaka ƙarfinsa. Da zarar ya jefa, zai ba da dama ga ‘yan wasa a nemo batirin.

    Nan fa ‘yan wasa za su bazama neman batiri. Burin kowa shi ne ya samo shi, sanan ya zo ya sanya shi cikin wannan ƙasa da mai dawa ya tara. Yayin da yaro guda ya samu, sauran yara za su bi shi da gudu cikin ƙoƙarin ƙwacewa daga hannunsa. A wannan yanayi, duk wanda ya ƙwace ya kawo cikin ƙasar mai dawa, to shi ya yi nasara.

    Wasu lokuta yaron da ya samu zai yi tamkar bai samu ba. Don haka zai ci gaba da yawo tamkar yana nema. A haka zai sanɗi sauran ‘yan wasan nan ya arce a     nakare zuwa wurin ƙasar mai dawa. Yayin da mutum ya samu nasarar sanya wannan batiri cikin ƙasar, shi ma ya zama mai dawa.

    5.28.2 Tsokaci

    Wannan wasa yana samar da nishaɗi ga yara. Sannan hanya ce ta motsa jiki gare su. Baya da haka, wasan na koya wa yara jarumta da dabarun ƙwatar kai. Domin sai yaro ya jure kuma ya yi amfani da hikimomi kafin ya kai ga sanya batiri cikin ƙasar mai dawa.

    WASANNI A ƘASAR HAUSA

    Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8. 


    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.