Dokin Kara

    5.30 Dokin Kara

    Wannan wasa ne na yara maza. Yara kimanin goma zuwa sama da haka ne suke taruwa domin gudanar da wannan wasa. Wasan ya kasance kwaikwayo ga hawan daba da sauran hawa makamantan wannan, da yara ke ganin manya suna gudanarwa. Ba ya tafiya da waÆ™a, amma akan bukaci kayan aiki yayin gudanar da shi.

    5.30.1 Wuri Da Lokacin Wasa

    i. Wannan wasa ba wuri guda ake gudanar da shi ba. Yawanci masu wasa sukan zaga unguwanni ne.

    ii. Akan gudanar da wannan wasa da hantsi ko da yamma.

    5.30.2 Kayan Aiki

    i. Karan dawa mai Æ™arfi

    ii. Æ˜yallaye

    iii. Æ˜usa

    iv. Igiya

    5.30.3 Yadda Ake Wasa

    Masu wasa sukan nemi kararen dawa masu Æ™arfi. Daga nan za su yanki gaÉ“oÉ“i daga jikin wani karan na daban, su yi amfani da Æ™usa su laÆ™a a jikin dogon kara mai Æ™arfi da suka samu a matsayin doki. Sai kuma su samo Æ™yallaye su yi wa dokin kwalliya. Akan yi amfani da igiya a matsayin linzami.

    Bayan nan yara sukan naÉ—a matsayi a tsakaninsu. Akan zaÉ“i sarki da galadima da waziri da wasu matsayin masu kama da wannan. Daga nan yara za su É—unguma a kan waÉ—annan dawakai su riÆ™a zagaya unguwanni. Wani lokaci sukan yi sukuwa, wani lokaci kuwa su tafi a hankali. WaÉ—anda suka yarda da Æ™arfin karan dawar da suke amfani da shi, sukan yi taÉ“arya. Wato su kafa karan a tsaye sannan su É—angalafe. Wasu kuwa dawakin suna karyewa a yayin da suka yi taÉ“arya.

    Haka yara za su ci gaba da yi har lokacin da suka gaji. Wani abin burgewa shi ne, masu wasan sukan bi umarnin sarki tamkar dai a hawan dawakin gaske.

    5.30.4 Tsokaci 

    Wannan wasa ne na motsa jiki ga yara. Sannan ya kasance tamkar hoton hango al’adar Bahaushe ta hawan dawaki. Yara sukan koyi halayya da É—abi’un shugabanci da lamuran da suka shafi fada.

    WASANNI A ƘASAR HAUSA

    Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.