Jirgi 1

    5.38 Jirgi 1

    Wannan na ɗaya daga cikin wasannin yara maza da ke da farin jini, da kuma ake samu a ƙasashen Hausa da dama. Kusan babu wata ƙasar Hausa da yara maza ba sa irin wannan wasa. Yaro guda ma zai iya yin wasan. Amma akan samu yara biyar zuwa sama da haka sun haɗu wuri ɗaya domin gudanar da shi.

    5.38.1 Wuri Da LokacinWasa

    i. Ana gudanar da wannan wasa ne a wurin da ke da sarari sosai. Wato kamar filin ƙwallo ko dai wani babban fili.

    ii. Akan yi wannan wasa da hantsi ko da yamma, musamman a lokutan da iska ke kaɗawa sosai.

    5.38.2 Kayan Aiki

    i. Leda

    ii. Dogon tsare

    iii. Tsinkaye masu kauri

    iv. Kara ko siririn itace

    5.38.3 Yadda Ake Wasa

    Yara sukan samu leda mai ɗan faɗi sannan marar ɓuli, sai su shimfiɗa ta ƙasa. Sai kuma su ɗora tsinkaye masu kauri bisa wannan leda. Waɗannan tsinkaye za su kasance masu matsakaicin tsawo, waɗanda kuma suka kai daga ƙarshe zuwa ƙarshen ledar. Yawanci tsinkayen sukan kasance uku ne. Guda biyu a kwance hagu zuwa dama, a sama da ƙasan ledar. Na ukun kuma sai ya kasance a bisansu, a tsakiya. Wato ya je daga sama zuwa ƙasan ledar a tsaye. Sai su ɗaure ƙarshen waɗannan manyan tsinkaye da jikin ledar ta kowane ɓangare.

    A ɓangare ɗaya kuma, za a tanadi dogon zare. Za a nannaɗe wannan zare jikin kara ko wani itace. Daga nan za a ɗaura bakin wannan zare a jikin ɗaya daga cikin kararen da aka ɗaura jikin leda. Idan aka yi haka, to jirgi ya haɗu ke nan.

    Yadda ake ta da jirgi kuwa shi ne, yaro zai ɗan jefa shi sama yayin da ya ware tsare kaɗan. Daga nan zai riƙa gudu wannan jirgi na bin sa. Sai kuma ya fara ware tsaren kaɗan-kaɗan. Yayin da yake sake warewa, iska za ta ci gaba da kaɗa jirgin zuwa sama. A haka har jirgin ya ɗan yi nisa sama. A irin wannan lokaci, yaro zai iya tsayuwa wuri guda ya ci gaba da ware tsarin. Iska kuwa za ta riƙa kaɗa wannan jirgi yana ƙara ɗaguwa sama. Abin gwaninta ne a ce jirgin yaro ya fi na abokansa nisa.

    5.38.4 Tsokaci

    Wannan wasa ne mai farin jini ga yara. Yana samar da nishaɗi da annashuwa gare su. Sannan yana taimaka musu wurin motsa jiki. Baya ga haka, wasan na buƙatar fasahar ƙirƙira.

    WASANNI A ƘASAR HAUSA

    Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.