Ticker

Karan Tsallake

5.39 Karan Tsallake

Wannan ma wasan yara maza ne wanda ke tattare da kasada. Misalin yara uku zuwa sama da haka ne suke gudanar da wannan wasa. Wasa ne wanda ba ya ɗauke da waƙa. Sai dai yana buƙatar kayan aiki yayin gudanar da shi. Wannan kayan aiki zai iya kasancewa igiya ko kara ko wani abu da za a riƙa tsallakewa.

5.39.1 Wuri Da LokacinWasa

i. Akan gudanar da wannan wasa a filayen wasanni, musamman na makarantu.

ii. Akan gudanar da wasan da hantsi ko da yamma. Ba a fiye yin sa da dare ba.

5.39.2 Yadda Ake Wasa

Yara biyu suka riƙe kara ko igiya. Kowanne daga cikinsu zai riƙe ƙarshe ɗaya, su ɗaga ta daidaitsawon da suka ƙiyasta za a riƙa tsallakewa. Sauran ‘yan wasa kuwa za su koma can nesa kaɗan. Daga nan za su riƙa zuwa ɗaya bayan ɗaya da gudu suna tsallake wannan kara ko igiya.

Duk wanda ya tsallaka zai yi murna da kuma tinƙahon nasara. Wasu kuwa sukan buge abin tsallakewar, ko ma su karya shi idan kara ne. Irin waɗannan akan ɗauke su a matsayin ragwaye.

5.39.3 Tsokaci

Wannan wasa ne na motsa jiki ga yara. Sai dai yana tattare da kasada. Yara da dama sukan ji ciwo a dalilin wannan wasa.

WASANNI A ƘASAR HAUSA

Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


Post a Comment

0 Comments