Ticker

    Loading......

Gori/Kodi 2 (Na Zamani)

 5.4 Gori/Koɗi 2 (Na Zamani)

Wannan wasa ne mai irin dokoki da sigar asalin wasan koɗi. Amma kayan aiki sun bambanta. Domin ana amfani ne da kayan aiki da zamani ya zo da su. Wato waɗanda suka kasance sabbi a muhallin Bahaushe.

5.4.1 Kayan Aiki

i. Marfin biro, musamman biro mai suna big da sauran biruka masu kama da wannan

ii. Faya-fayen kan batirin rediyo babba

iii. Kan biro da aka cire daga jikin hanjin biro

 

5.4.2 Yadda Ake Gudanar Da Wasa

Akan samu marfin biro, sai a ɓalle ɗan dogon mariƙa da yake zuwa da shi. Daga nan za a nemi batira manya na rediyo, a fasa, a cire faya-fayen roba da ke samansu. Sai a zura wannan marfin biro cikin ɓulun da ke tsakiyar waɗannan faya-fayen saman batir. Wani abin burgewa shi ne, da zarar faifayin ya je ƙarshen marfin biron, to zai riƙe ɗamar. Akan sanya faya-faye biyu ko uku ko ma huɗu a jikin marfin biro ɗaya. Daga nan za a riƙa amfani da shi a matsayin koɗi. Wani lokaci akan cire kan biro (wurin rubutun) daga jikin hanjinsa. Sai a yanke ƙarshen tsinin marfin biron, daidai da yadda za a iya cusa wannan kan biro (da aka cire daga jikin hanji). Daga nan za a cusa shi ya zauna daidai. Dokokin wasan kuwa suna kan kamar yadda aka yi bayaninsu a sama. Wato daidai suke a wasan koɗi na gargajiya.

 

5.4.3 Tsokaci

A zuwa yau, hanyoyin samar da koɗi na zamani sun ƙara bunƙasa. Akan yi amfani da marfin gorar man keken ɗinki a matsayin koɗi. Wanda da ma yana da siffar koɗi tun asali, saboda haka, gyara kawai za a ɗan masa. Sannan akan yi amfani da robar jikin kan sirinjin ɗin allura. Sai a karye wurin ƙarfen kawai. Wannan ƙaramar roba ita za a cusa a tsakiyar marfin gora (kamar gorar fanta ko koka-kola ko faro da makamantansu), bayan an samar da ɓuli a tsakiyar marfin gorar ta hanyar amfani da wani abu mai tsini da ƙarfi.

WASANNI A ƘASAR HAUSA

Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


Post a Comment

0 Comments