Danda Dokin Kara

    5.47 Danda Dokin Kara

    Wannan wasan maza ne da ke cikin rukunin wasannin tashe. Yana tafiya da waÆ™a. Sannan yana da buÆ™atar kayan aiki domin gudanarwa. Kimanin mutane biyar ne zuwa sama da haka suke gudanar da wannan wasa.

    5.47.1 Wuri Da LokacinWasa

    i. Masu wasa sukan bi shaguna da wuraren da mutane ke taruwa da kuma gidaje domin gudanar da wannan wasan tashe.

    ii. An fi gudanar da wannan wasa da hantsi ko da yamma. Wato dai saÉ“anin mafi yawan wasannin tashe da ake gudanarwa da dare bayan an sha ruwa.

    5.47.2 Kayan Aiki

    i. Karan dawa mai Æ™arfi da kauri

    ii. Æ˜yallaye

    iii. Babbar riga/malum-malum

    iv. Rawani

    v. Igiya (a matsayin linzami)

    5.47.3 Yadda Ake Wasa

    Yara za su samu karan dawa mai Æ™arfi da kauri su É—aÉ—É—aura masa Æ™yallaye a matsayin doki. Za su yi haka cikin kwaikwayon yadda ake kwalliyar doki. ÆŠaya daga cikin yaran kuma zai yi shiga irin ta sarauta. Wato zai sanya babbar riga ya sha rawani, sannan ya hau wannan dokin kara.

    Yayin da aka iso wurin tashe yaron da ke bisa dokin zai riÆ™a waÆ™a, sauran yara kuma na amsawa. WaÆ™ar kuwa ita ce:

    Bayarwa: Assalamu alaikum kun yi baÆ™o,

    Amshi: Ga danda dokin kara.

     

    Bayarwa: Masu gidan nan kun yi baÆ™o,

    Amshi: Ga danda dokin kara.

     

    Bayarwa: Sai ku ban kaji bakwai daÆ™wale,

    Amshi: Ga danda dokin kara.

    Bayarwa: Da tuwon shinkafa da miya ja,

    Amshi: Ga danda dokin kara.


    Bayarwa: Sai ku ban soyen nama na rago,

    Amshi: Ga danda dokin kara. 

    5.47.4 Tsokaci

    Wannan wasa kwaikwayo ne ga shigar sarauta da kuma al’adar Bahaushe na yi wa doki kwalliya. Sai dai an shirya shi ne kawai domin nishaÉ—antarwa. Idan ba haka ba, ina aka taÉ“a ganin sarki da kwaÉ—ayi?

    WASANNI A ƘASAR HAUSA

    Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.