Maiƙiriniya

    5.49 Maiƙiriniya 

    Wannan ma wasan tashe ne na yara maza. Kimanin yara huɗu ne zuwa sama da haka ke gudanar da shi. Yana tafiya da waƙa wadda ta fi kama da magana. Wato ba rera ta ake yi cikin raujin murya ba. Sannan ba a buƙatar kayan aiki yayin gudanar da shi. Sai dai a wasu lokutan ɗaya daga cikin yaran da ake kira; ‘Mai Ƙiriniya,’ na shafa bula ko wani abu makamancin wannan a fuskarsa. Kamar sauran wasannin tashen ƙasar Hausa, akan gudanar da wasan Maiƙiriniya bayan an sha ruwa.

    5.49.1 Yadda Ake Wasa 

    Yara sukan taru, sannan su zaɓi ɗaya daga cikinsu wanda ke da wayo sosai a matsayin Maiƙiriniya. Kamar yadda sunansa ya nuna, yaron na fitowa ne a matsayin wanda ke da matuƙar ƙiriniya ta wuce ƙima. Shi ne zai wuce gaba, sauran yara na biye.

    Yayin da aka isa wurin tashe, yara za su fara ba da waƙa, Maiƙiriniya kowa na amsawa. Ga yadda waƙar ta ke

    Yara: Maiƙiriniya,

    Maiƙiriniya: Eye.

     

    Yara: Wa ya sa ka ne?

    Maiƙiriniya: Baba.

     

    Yara: Maiƙiriniya,

    Maiƙiriniya: Eye.

    Yara: Wa ya sa ka ne?

    Maiƙiriniya: Mama.

     

    Yara: Mai Ƙiriniya,

    Maiƙiriniya: Eye.

     

    Yara: Wa ya sa ka ne?

    Maiƙiriniya: Kawu.

     

    Yara: Maiƙiriniya,

    Maiƙiriniya: Eye.

     

    Yara: Wa ya sa ka ne?

    Maiƙiriniya: Baffa.

     

    Yara: Maiƙiriniya,

    Maiƙiriniya: Eye.

     

    Yara: Wa ya sa ka ne?

    Maiƙiriniya: Gwaggo.

     

    Yara: Maiƙiriniya,

    Maiƙiriniya: Eye.

     

    Yara: Wa ya sa ka ne?

    Maiƙiriniya: Inna.

     

     

    Yara: Mai Ƙiriniya,

    Maiƙiriniya: Eye.

     

    Yara: Wa ya sa ka ne?

    Maiƙiriniya: Adda.

     

    Yara: Maiƙiriniya,

    Maiƙiriniya: Eye.

     

    Yara: Wa ya sa ka ne?

    Maiƙiriniya: Yaya

     

    Yara: Maiƙiriniya,

    Maiƙiriniya: Eye.

     

    Yara: Wa ya sa ka ne?

    Maiƙiriniya: Kaka. 

    Yayin da ake wannan waƙa, Maiƙiriniya zai riƙa aikinsa na ƙiriniya. Duk abin da ya samu zai ɗauka. Idan a cikin gida ne. Zai riƙa tattare irin su butoci yana canza musu wuri. Wani lokaci zai riƙa faman cire bishiya ko ya rungumi ginin ɗaki da nufin zai ɗaga shi. Wani lokaci kuwa ya ɗaga Katanga ya riƙa turawa har da nishi da botso da nufin zai ture ta. Kai, ƙiriniyar dai ta kai ƙiriniya.

    5.49.2 Tsokaci

    Wannan wasa na kundace sunayen dangi na jini. Kamar dai yadda Maiƙiriniya ke lissafo waɗanda suka sanya shi wannan aiki da yake yi, duk da ma sharri yake kwantara musu. Wasan na samar da nishaɗi ƙwarai ga masu kallo. An gina shi kan raha da ban dariya. Yo kai Mai Ƙiriniya, idan ka ɗauki ɗakin ina za ka kai shi?

    WASANNI A ƘASAR HAUSA

    Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.