Langa

     5.5 Langa 

    Wannan ma wasa ne da yara maza suke gudanarwa. Yawanci yara daga shida zuwa sama ne suke gudanar da langa.

     

    5.5.1 Lokaci Da Wurin Wasa

    i. An fi gudanar da wannan wasa da dare, musamman lokacin da akwai farin wata.

    ii. Sanannen wurin gudanar da wasan langa shi ne dandali.

     

    5.5.2 Yadda Ake Gudanar Da Wasa

    Yara sukan rabu zuwa ƙungiyoyi biyu. Misali kamar yara biyar-biyar a kowane rukuni. Wani lokaci kuma yakan kasance ɗaya daga cikin rukunnen ya ƙunshi yaran da suka zarce yawan ɗaya abokan karawar su. Hakan na faruwa ne yayin da aka tara masu iyawa ko manya (mafiya ƙarfi) a rukuni ɗaya. Saboda haka, ɓangaren da ba su iya sosai ba, ko suka fi ƙanƙanta, sai a ba su yara da yawansu ya zarta  rukunin masu ƙwarewar. Irin waɗannan rukunne ana ce da su gari.

     

    Kowa zai ɗana lako. Daga nan ‘yan garin ruwa za su tambayi abokan karawar su; “Kun shirya?” Idan sun shirya za su amsa da: “Eh!” Daga nan ‘yan garin ruwa za su ce: “Ruwa ta bayar.” Da furta haka za a fara fafatawa. Burin abokan karawar ‘yan garin ruwa shi ne su kasha ruwa. ‘yan garin ruwa kuwa za su yi ta ƙoƙarin kare ruwa. Ruwa kuwa za ta yi ta ƙoƙarin tsinkewa domin ta sha.

     

    Haka za ai ta gwaɓzawa har sai ko ruwa ta sha ko an kasha ruwa ko an yi jaga ko kuma an yi zubel. Daga nan kuma sai a juya gari idan ruwan ‘yan garin ruwa ya ƙare. Wannan ya danganta da dokar wasan, ko dai ta kasance ruwa ɗaya, ko ruwa biyu ko ruwa uku ko makamancin haka.

     

    5.5.3 Wasu Daga Cikin Dokokin Langa

    Duk da cewa dokokin langa na samun canji daga wasa zuwa wasa, akwai wasu fitattun dokoki na wasan langa kamar haka:

    i. Duk wanda lakonsa ya tsinke ko ya (lakon) taɓa ƙasa to ya mutu.

    ii. Ba a fara wasa sai ruwa ta bayar.

    iii. Yayin da aka yi jaga, ‘yan garin ruwa sun samu maki biyu a maimakon ɗaya.

    iv. Gula ko ƙulli ƙeta ce a langa.

    v. Da zarar an kashe ruwa, to wasa ya ƙare.

    vi. Kowa tilas ya dakata yayin da aka kira saranda.

     

    5.5.4 Tsokaci

    Wasan langa kwaikwayo ne ga yaƙi. Ruwa ta kasance tamkar sarki a yaƙi, yadda idan aka kasha sarki, to kuwa an ci galaba a yaƙi. Haka ma ‘yan garin ruwa ke ƙoƙarin kare ruwa tamkar yadda mayaƙa ke ƙoƙarin kare sarkinsu a filin daga. Langa tana temaka wa yara wurin motsa jiki. Sannan tana ƙara musu jarumta da ƙarfin jiki. Sannan tana koyar da su dabarun kare kai da na neman hanyoyin tsira.

    WASANNI A ƘASAR HAUSA

    Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.