5.5.2 Lansika

     

    Citation: BunguÉ—u, U.H. (2021). Bara da wasu waÆ™oÆ™in bara a Æ™asar HausaAhmadu Bello University Press Limited.

    Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

    Dr. Haruna Umar BunguÉ—u
    (Sarkin Gobir Na BunguÉ—u)
    Email: harunaumarbungudu@gmail.com
    Phone: 08065429369

    Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar Hausa

    5.5.2 Lansika

     Jagora: Lansika, inna lansika.

     Amshi: Kulle.

     Jagora: Mata dangin Fatima.

    Amshi: Kulle.

     Jagora: Ku taru ku bamu na Annabi.

    Amshi: Kulle

    Jagora: Mata dangin Fatima.

    Amshi: Kulle.

    Jagora: Ku taru ku bamu na Annabi.

    Amshi: Kulle.

    (Mata Dangin Fatima)

    Ita ma wannan waÆ™a kalmar “kulle” ita ce amshinta. Kalmar kulle ba ta É—auke da wata ma’ana da aka sani a harshe wadda za a ce ga abin da take nufi, don haka ita ma kalmar amshi ce maras ma’ana. A lura da cewa rubutattun waÆ™oÆ™in da ake amfani da su wajen bara, mabarata na Æ™oÆ™arin su sama masu amshi ko da ba su da shi. Haka na faruwa a cikin taro ko a kaÉ—aice. Misali, a waÆ™ar Imfiraji mabarata na yi mata amshi da:

     Mai sadaka Ala karÉ“a,

     Ala sa mu ga shugaban Ma’aika.

    Haka ma sauran waƙoƙi mabarata kan yi ƙoƙari su sa mata amshi wanda zai yi daidai da baransu.


    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.