Dantsoho Mai Cin Bashi

    5.55 ÆŠantsoho Mai Cin Bashi

    Wannan wasarntashe ne na yara maza. Kimanin yara biyar zuwa sama da haka ne suke gudar da wannan wasa. Sannan akan bukaci kayan aiki yayin gudanar da shi. Kamar yadda mafi yawan wasannin tashe suke, an fi gudanar da wannan wasa da dare.

    5.55.1 Kayan Aiki

    i. Kayan sawa na dattawa kamar babbar riga da hula da rawani

    ii. Matashin kai/filo

    iii. Sanduna guda biyu

    iv. Igiya ko zane

    5.55.2 Yadda Ake Wasa

    ÆŠaya daga cikin yara zai yi shigar dattijo. Wato zai sanya babbar riga da hula da rawani, sannan ya riÆ™e sandan dogarawa. Za kuma a goya wawannan yaro filo a bayansa ta cikin wannan babbar riga. Akan É—aure filon tamau da igiya ko zane yadda ba zai kwance ba. Wannan shi ake kira ÆŠantsoho a cikin wasan. Da yake kuma babbar rigar ta rufe shi, sannan yaron a sunkuye zai riÆ™a tafiya a matsayinsa na tsoho, ba dole ne a gane akwai filo goye bayansa ba. Wani kuma daban daga cikin yaran zai riÆ™e sanda a hannunsa.

    Yayin da aka je wurin tashe, yara za su riÆ™a faÉ—i a tare:

    “Kai É—an tsoho mai cin bashi, biya mu kuÉ—in bashinmu na bara.”

    Da zarar sun faÉ—i haka, wanda ke riÆ™e da sanda zai dubi bayan tsoho ya tima masa sanda. Sai dai ka ji ‘tim.’ Mai kallo sai ya ji ras a zuciya, ganin yadda ake bugun wannan ÆŠantsoho. ÆŠantsoho kuwa zai riÆ™a ihu yana cewa:

    “Wayyo Allah za su kashe ni. Ku ba ni in ba su.”

    5.55.3 Tsokaci

    Wannan wasa yana samar da nishaÉ—i musamman ga masu kallo. Sannan yana shaguÉ“e ga mai wani hali, wato cin bashi. Mai cin bashi na banza da wofi dai kullum yana cikin wulaÆ™anci kamar yadda ÆŠantsoho ya tsinci kansa a ciki. Sai dai an gina wasan kan raha da ban dariya. Domin ko ba komai, ÆŠantsoho akwai taurin rai.

    WASANNI A ƘASAR HAUSA

    Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.