5.6.1 Laƙad raliyal Lahu

     Citation: Bunguɗu, U.H. (2021). Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar HausaAhmadu Bello University Press Limited.

    Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

    Dr. Haruna Umar Bunguɗu
    (Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
    Email: harunaumarbungudu@gmail.com
    Phone: 08065429369

    Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar Hausa

    5.6.1 Laƙad raliyal Lahu

    Jagora: Laƙada raliyallahu anal muminina.

    Amshi: To.

    Jagora: Angal lahu angaruhin mu’asha.

    Amshi: To.

    Jagora: An aiko mu inda malam mu gan shi.

    Amshi: To.

    Jagora: Ga shi biki gare shi mi zamu ba shi.

    Amshi: To.

    Jagora: Kai ka mukai mu samu lada cikakka.

    Amshi: To.

     (Laƙada Raliyallahu)

    A cikin wannan waƙa akwai wata jumla a ɗa na byu mai cewa “Angal lahu angaruhin mu’asha”. Wannan ɗan waƙa ba ya da wata ma’ana, amma idan mai sauraro ba mai ilmi ba ne sai ya ji kamar wata aya ce ake karantowa. Wannan wani surkulle ne da mabarata ke amfani da shi a cikin waƙoƙinsu domin su nuna wa mai sauraro kamar su masu ilmi ne suna cirato ayoyi suna sakawa a cikin waƙensu. Haka ma “Lanzika inna Lanzika” a cikin waƙar “mata dangin Fatsima” shi ma surkulle ne mai kama da ana karanto wani abu mai wata ma’ana da ta danganci karatu na addini kamar dai yadda wani mutum kan ce “Waman takanahu illa awaya”. Da sauransu.


    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.