Robali/Kyauro - ‘Yar Jifa

    5.61 Robali/Kyauro

    Wannan wasa ne na yara maza. Yana cikin jerin wasannin da ba sa tafiya da waƙa. Daga cikin kayan aikin da ake amfani da su kuwa akwai robali. Ba a ƙayyade wani lokaci ba na yin wannan wasa. Sai dai ba a yin sa sai idan akwai wadataccen haske. Hasken farin wata ba ya wadatarwa ga wannan wasa. Saboda haka, idan da dare za a yi, dole ne ya kasance a kusa da ƙwan lantarki mai haske. Wannan ya sa aka fi yin wasan lokacin da ido ke gani.

    5.61.1 Yadda Ake Wasa

    Akasari a lokacin da ake yayin robali, yara da yawa sukan saya su sanya a hannayensu. Wasu kuma sukan sanya ne a leda ko cikin aljihu. Abin tinƙaho ne ga yaro yayin da robali suka cika hannunsa, wato nasa ya fi na kowa yawa. Sannan robalin daraja-daraja ne; domin kuwa wanda yake da kala ya fi wanda ba shi da shi daraja. Masu kala dai su ne ja ko kore. Marar kala kuwa shi ne ruwan ƙasa.

    Manyan hanyoyin samun robali ga yara guda uku ne. Na farko dai shi ne saya a kantuna ko dandali wurin da ake sayar da su. Hanya ta biyu kuwa ita ce kyauta. Wato yayin da wani yaro ya bushi iskar ba wa abokinsa kyautar robali. Hanya ta uku kuwa ita ce tatikewa daga hannun wasu ta hanyar wasa. Ɗaya daga cikin wasannin da ke ba wa yara wannan dama shi ne ‘yar  taru. 

    Yadda ake wannan wasa shi ne, masu wasa za su nemi wani wuri su ajiye robali guda ɗaya a ƙasa. An fi ajiyewa a kan siminti. Akan kira wannan robali da aka ajiye a ƙasa tirke. Daga nan yara za su ja baya, su ba da tazara daga wurin da aka kafa turke. Za a yi amfani da ƙafa a ja layi guda ɗaya. A kan layin ne duk wani mai wasa zai tsaya. Sannan za a riƙa jefa robali ɗaya bayan ɗaya zuwa wurin da aka kafa tirke. Burin kowane mai jefawa shi ne robalinsa ta hau kan ɗaya daga cikin waɗanda aka riga aka jefa.

    Yayin da duk robalin wani ta hau kan ɗaya daga cikin waɗanda aka jefa, to zai je ya kwashe dukkanin robali da ke ca. Tirke kaɗai zai bari. Salon jefa robali iri-iri ne. Akwai masu jifa, wato a ɗora shi bisa tafin hannu sai kuma a wurga. Akwai kuma masu harbi. Wannan salo ne na gwanaye. Sukan ɗame robali ɗin jikin yatsunsu. Ƙarshensa nakan yara manuniya, ɗaya gefen kuma an tare shi da babbar yatsa. Da zarar an kautar da babbar yatsar, robali zai tafi da gudu kamar an harba shi. A irin wannan wasa, wanda ya fi iyawa ko ya fi samunsa yaya kan tatike robali na mutane da dama.

    5.61.2 Wasu Daga Cikin Dokokin Wasa

    i. Wanda ya yi sunkuyo to ko ya ci ba za a ba shi ci ba. A maimakon haka, za a je ne kawai a sauke ta daga kan ci da ta yi, a kuma ci gaba da wasa.

    ii. Idan wasan ‘yar iyaka ce, za a ja wani layi da ke nuna iyakar wurin da ake so mutumya ci a ciki. Saboda haka, ko da mutum ya jefa robali bisa wani da aka riga aka jefa, amma wajen iyaka, to bai ci ba.

    iii. Yayin da ake kokonto cewa wanda ya yi jifa ya ci ko bai ci ba, to za a je a duba. Idan aka ga akwai kafa da ya samu tsakanin robalin da ke ƙasa da wanda aka jefo kansa, to mai jifa ya ci. Idan babu kafa kuwa (ya dai ɗan ɗoru ne kawai kansa) to bai ci ba. Wannan kafa akan kira ta rami.

    iv. Wanda robalinsa suka ƙare zai iya karɓar aro domin ya yi jifa. Idan ya samu sa’ar ci, to zai mayar wa wanda ke bin sa bashi adadin waɗanda ya ara.

    v. Mai wasa zai iya ba wa wani daga cikin ‘yan wasa kyautar robali yayin da nasa suka ƙare.

    WASANNI A ƘASAR HAUSA

    Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.