6.1 Caccayya - Daga Littafin WAƘOƘIN HAUSA NA GARGAJIYA (Page - 132)

    Citation: Gobir, Y.A. & Sani, A-U. (2021). Waƙoƙin Hausa Na Gargajiya. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-0-01.

    6.1 Caccayya

    Wannan Waƙa ce da yara maza da mata duka ke gudanarwa. Lokacin damina ake wannan waƙa. Domin kuwa akan fara ne yayin da hadari ya taso aka fara kaɗa iska da ke nuna alamar za a yi ruwa. Ba ta da takamaiman lokacin da aka keɓe domin gudanar da  rera ta. A lokacin da hadarin ya taso, yara sukan fito ƙofar gida, ko dandali. Za su fara waƙa da tsalle da tafi tare da buga ƙafafu a ƙasa. Wani lokaci za su ɗunguma cikin wannan yanayi su zaga kwararo-kwararo a cikin unguwa. Wasu daga ciki za su riƙa ba da waƙar, wasu kuwa na amsawa. Ga yadda waƙar take:

    Bayarwa: Allah ba mu ruwa,

    Amshi: Caccayya.

     

    Bayarwa: Gona ta jiƙe,

    Amshi: Caccayya.

     

    Bayarwa: Dawa ta jiƙe,

    Amshi: Caccayya.

     

    Bayarwa: Gero ya jiƙe,

    Amshi: Caccayya.

     

    Bayarwa: Masara ta jiƙe,

    Amshi: Caccayya.

     

    Bayarwa: Maiwa ta jiƙe,

    Amshi: Caccayya.

     

    Bayarwa: Wake ya jiƙe,

    Amshi: Caccayya.

     

    Bayarwa: Kuɓewa ta jiƙe,

    Amshi: Caccayya.

     

    Bayarwa: Mu ma mu jiƙe,

    Amshi: Caccayya.

     

    Bayarwa: Kowa ya jiƙe,

    Amshi: Caccayya.

     

    Bayarwa: Allah ba mu ruwa,

    Amshi: Caccayya.

    Haƙiƙa wannan waƙa na samar da nishaɗi ga yara. Da ma dai lokacin da hadari ya taso, sannan iska na kaɗawa, akan samu yanayi mai daɗi. Babba ma da zai samu sake, to kuwa da sai ya yi ta tsalle cikin wannan yanayi. Waƙar da yaran ke rerawa kuwa na ƙunshe da jigon roƙon ruwa.

    WAƘOƘIN HAUSA NA GARGAJIYA

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.