6.10 Wasar Gora-Gora
Wannan ma wasan ‘yanmata ne. Bai zama tilas a samu mutane da yawa ba domin gudanar da shi. Yara biyu ma kacal za su iya. Sai dai idan suka fi hakan abin ya fi armashi. Akan yi wasan da dare. Sai dai a ɗaiɗaikun lokuta ba za a rasa ba da ake yi da hantsi ko da yamma. Ba a buƙatar wasu kayan aiki na musamman domin gudanar da wannan wasa. Sannan akan yi wasan a filin ƙofar gida, har ma a cikin gida wasu lokutan.
6.10.1 Yadda Ake Wasar Gora-gora
‘Yanmatan kan yi layuka biyu, suna fuskantar juna. Wato kowacce da wata a gabanta suna kallon juna. Daga nan za a samu jagora mai yin waƙa (idan sun wuce biyu). Idan su biyu ne kuwa, ɗaya daga cikinsu sai ta riƙa yin waƙar. Yayin da ta gaji, sai ɗayar ta karɓa. Za su riƙa tafa hannaye tare da ɗora ɗaya hannun a ƙirji. Ma’ana, yayin da suka tafa da hannun dama, to za su ɗora na hagu a ƙirji. Idan kuwa da hannun hagu suka tafa, sai su ɗora na dama a ƙirji. Za su ci gaba da haka cikin sauri da ƙwarowa, ba tare da kuskure ba. Wannan ya sanya ‘yan wasa dole su natsu tare da mayar da hankali, gudun yin kuskure.
6.10.2 Waƙar Wasa
Gora-gora,
Goran Iya da Baba,
Sun taru suna zagina,
Suka ce ba zan rama ba.
Na zagaya ban ɗaki,
Na tad da matar sarki,
Ɗaya da ciki ɗaya,
Da goyon ɗan zakara.
Ke wannan wa ya yi maki ciki?
In ba ki magani ya zube,
Zube ɗan farkan nan!
Zube ɗan farkan nan!
6.10.3 Tsokaci
Wannan wasa hanya ce ta motsa jiki. Sannan za a iya hasashen ɓirɓishin zancen cikin shege da zubarwa daga waƙar wasan.
Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.