To Iya

    6.100 To Iya

    Wannan ma wasan tashe ne na yara mata. Sukan gudanar da shi da dare bayan an sha ruwa a watan azumi. Sannan sukan bi gida-gida ne domin gudanar da wasan. Yana kuma buÆ™atar kayan aiki yayin gudanar da shi. Kimanin yara biyar ne zuwa sama suke gudanar da wannan wasa. Daga cikinsu akwai mai fitowa a matsayin uwa, da kuma ake kiranta iya. Sai kuma sauran ‘yan wasa da suke kasancewa a matsayin ‘ya’yanta.

    6.100.1 Kayan Aiki

    i. Tabarma ko tabarmi

    ii. Filo/matashin kai

    iii. Kwanoni da wasu shirgi

    iv. Zane ko kallabi babba da ake amfani da shi wurin É—aure faggon kayan

    6.100.2 Yadda Ake Wasa

    Yara sukan nemi tabarma da filo/matashin kai da wasu tarkace kamar kwanoni da makamantansu. za su ka su nemi zane ko babban kallabi su É—aure su wuri É—aya. Daga nan yaran za su É—unguma wurin tashe. ÆŠaya daga cikinsu, wadda ta fi su girma a mafiyawan lokuta, za ta kasance uwarsu a cikin wasan. Sauran kuwa duka ‘ya’yanta ne. Saboda haka za su riÆ™a kiran ta da iya ita kuwa za ta kira su da ‘ya’yana.

    Yayin da suka isa wurin da za su yi tashe, yara za su aje faggon da suka taho da shi. Sai kuma iya ta fara faman tattare-tattare tamkar dai wadda take faman haÉ—e kayanta wuri É—aya domin tafiya wani wuri. Za ta riÆ™a yi tana waÆ™a. ‘ya’yan nata kuwa za su riÆ™a amsawa. Ga yadda waÆ™ar take:

    Iya: Ku zo ku zo ‘ya’yana,

    Ya’ya: To iya.

     

    Iya: Ubanku ya koro ni,

    Ya’ya: To iya.

     

    Iya: Saboda babbar loma,

    Ya’ya: To iya.

    Haka za su ci gaba da wannan waÆ™a. Yayin da ta kamala tarkata faggonta, za ta kinkime su. Sannan za ta ci gaba da kaÉ—a kan ‘ya’yan da nufin su tafi. Wato dai tamkar wadda mijinta ya kora da gaske.

    6.100.3 Tsokaci

    Wannan wasa na samar da nishaÉ—i ga masu gudanarwa da kuma musamman masu kallo. Sannan akwai É“irÉ“ishin nuna wani yanayi da aure kan shiga, a Æ™asar Hausa. Wato ko dai yaji ko saki. An gina waÆ™ar wasan bisa raha. Lallai riÆ™on Iya sai hukuma tun da manyan loma har na sa a kore ta.

    WASANNI A ƘASAR HAUSA

    Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.