Ni Karkashi

    6.101 Ni Karkashi

    Wannan wasa ne na yara mata da ke cikin rukunin wasannin dandanli. An fi gudanar da shi da dare, musamman lokacin farin wata. Yara biyu ne suke gudanar da wannan wasa. Saboda haka, idan masu wasa suna da yawa, kowacce za ta haÉ—u da abokiyar wasa guda. Wasan na tafiya da waÆ™a, amma ba ta buÆ™atar wani kayan aiki yayin gudanar da shi. Yana kuma É—aya daga cikin wasannin tsaye. 

    6.101.1 Yadda Ake Wasa

    Yara za su juya wa juna baya. Sai kuma su sanya hannuwa cikin najuna. Wato kowacce za ta kasance rungume da hannuwan ‘yaruwarta, amma ta baya. Sai kuma su fara goye-goye a haka nan. Wato É—aya za ta sunkuya ta janyo abokiyar wasanta yadda abokiyar wasan za ta kasance kwance kan bayan wadda ta janyo ta, kamar dai goyon kuwa. Sai kuma ta sauke ta. Ita kuma waccar ta yi haka nan. Za su riÆ™a waÆ™a yayin da suke wannan goye-goye kamar haka:

    Bayarwa: Ni karkashi,

    Amshi: Ni lalo.

     

    Abayarwa: Mijina,

    Amshi: Matata.

    6.101.2 Tsokaci

    Wannan wasa na samar da nishaÉ—i ga yara. Sannan hanya ce ta motsa jiki gare su. Bayan haka, wasan na nuni ga dangantakar da ke tsakanin miji da mata, ta Æ™ut-da-Æ™ut.

    WASANNI A ƘASAR HAUSA

    Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.