Tabarya

    6.103 Taɓarya

    Wannan ma wasan yara mata ne. Babu wani ƙayyadadden wuri da lokaci da aka fi gudanar da wannan wasa. Akan yi wasan a ko’ina sannan a kowane lokaci. Kayan aikin da ake buƙata shi ne zaren buhu. Ba ya tafiya da waƙa, sannan takan kasance a zaune ko a tsaye.

    6.103.1 Yadda Ake Wasa

    Yara na samun zaren buhu mai ɗan madaidaicin tsayi; sai su ɗaure bakinsa. Ma’ana dai za su haɗe bakin zaren su ɗaure.  Za kuma su siƙe zaren da hannu biyu (hagu da dama). Daga nan ne kuma za su riƙa sarrafa zaren da yatsun hannunsu. Yanayin sarrafawar ya dangata da abin da yaran ke son haɗawa.

    Akan haɗa abubuwa iri-iri da wannan zare. Daga cikinsu akwai:

    a. Taɓarya

    b. Kwabo

    c. Kasuwar ƙudaje

    d. Kwabo a bayan banki

    e. Tsohuwa ta hau mota

    f. Gadan jaɓa

    6.103.2 Tsokaci

    Wannan wasa na samar da nishaɗi ga yara. Sannan yana buƙatar amfani da hikima da basira. Yayin da mutum ya sa wa yaran da ke wannan wasa ido, zai yi mamakin yadda suke sarrafa zaren da yatsunsu, har su samar da wani abu mai wata siffa sananniya.

    WASANNI A ƘASAR HAUSA

    Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.