Mai Ciki

    6.12 Mai Ciki

    Wannan ma wasan tashe ne da ake gudanarwa cikin watan azumi. Yara shida zuwa sama da haka ke gudanar da wannan wasa. A cikinsu akan samu mai ciki (wadda za a yi wa cikin tsumma) da kuma shugabar wasa, wato mai ba da waÆ™a. An fi yin wannan tashe da dare, bayan an sha ruwa. Sukan bi gida-gida domin gudanar da wasan.

    6.12.1 Kayan Aiki

    i. Tsummokara

    6.12.2 Yadda Ake Wasar Mai Ciki

    Za a sanya wa Mai Ciki tsummokara a cikin riga, ya yi girma tamkar mai ciki. Sannan a É—aure sosai yadda ba zai kwance ba yayin wasa. Yayin da suka shiga cikin gida, za ta kasance a gaba. Za ta riÆ™a tafiya da Æ™yar irin ta masu ciki, tare da É—ora hannu a baya (dafe baya da babban Æ™arewa). Daga nan jagora za ta fara waÆ™a saura suna amsawa. Mai Ciki kuwa tana ta fama da ciki.

    6.12.3 Waƙar Mai Ciki

    Jagora: Iye ga ni nan tafe.

    ‘Y/Amshi: Mai ciki

     

    Jagora: Iye ga ni nan tafe.

    ‘Y/Amshi: Mai ciki

     

    Jagora: Wallahi ba ni son sunan nan!

    ‘Y/Amshi: Mai ciki

     

    Jagora: Sunan uwar mijina ke nan.

    ‘Y/Amshi: Mai ciki

     

    Jagora: Wallahi za mu É“ata da mutum!

    ‘Y/Amshi: Mai ciki

     

    Jagora: Wallahi har gaban alÆ™ali!

    ‘Y/Amshi: Mai ciki

     

    Jagora: Wallahi ba ni son sunan nan!

    ‘Y/Amshi: Mai ciki

    6.12.4 Tsokaci

    Wannan wasa ya kasance tamkar madubin hango rayuwar mai ciki. Yana samar da nishaÉ—i Æ™warai ga masu kallo, musamman ganin yadda yara ke kwaikwayon mai ciki. Sannan yana nuna al’adar Bahaushe ta tsolayar mai ciki, duk da cewa cikin abin farin ciki da alfahari ne.

    WASANNI A ƘASAR HAUSA

    Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.