Babunna

    6.18 Babunna 

    Wannan wasan yana kama da Ɗan Balum-balum a sigar aiwatarwa. Amma waƙar ciki ta bambanta. Yara misalin huɗu zuwa sama da haka ne suke gudanar da wannan wasa.

    6.18.1 Wuri Da Lokacin Wasa

    i. Asalin wasan na dandali ne, amma akan yi shi a wurin da aka samu taron yara. Kamar wurin niƙa ko wurin talla ko sana’a.

    ii. Akan gudanar da wasan da hantsi ko da yamma ko da dare. Wasan dare an fi yin sa a dandali.

    6.18.2 Yadda Ake Gudanar Da Wasa

    Yara sukan tsaya a layi ɗaya. Fes za ta fito gaba ta riƙa fuskantarsu. Daga nan za a fara wasa ta hanyar tsalle da tafi. Za a fara ƙirge daga biyar zuwa ɗari. Sai dai bayan an ambaci biyar da goma, za a riƙa tsallake goma-goma. Ke nan gomiya kawai za a riƙa ambata (goma, ashirin, talatin …) har zuwa ɗari. Fes za ta ‘fuskanci ta farko a cikin layi ne domin su fara. Yayin da aka ƙwace ta, to za ta koma cikin layi, daidai wurin da wadda ta ƙwace take tsaye. Wadda ta ƙwace kuma za ta dawo gaban layi, wato dai yin ta ya zo.

    Kafin a ƙwace ko a ci nasara, dole ne sai an yi kaɗi uku. Yayin da masu kaɗi suka ware sau uku a tare ko suka tsuke sau uku tare, to an ƙwace mai yi. Idan kuwa aka samu saɓani a yayin ɗaya daga cikin kaɗin guda uku, to mai yi ta ci nasara. Sai ta wuce zuwa yarinya ta gaba. Ga misalin yadda abin yake:

    Babunna,

    Gomanna,

    Ishina,

    Talana,

    Arbana,

    Hamsana,

    Sittana,

    Sabana,

    Tamana,

    Casana,

    Riɗana.

     

    Yayin da mai yi ta tsallake dukkanin waɗannan, to ta yi randa ɗaya ke nan. Fitarta ta danganta da randa nawa ake yi a wasan. Ko dai randa ɗayan, ko biyu ko sama da haka. Da zarar an gama gaba ɗaya, wato kowa ta fita saura guda ɗaya, to za a kaɗa wan tu fayif (1,2,5). Wannan kaɗi zai iya kasancewa ‘yar zubel ko ba ‘yar zubel ba. Wacce ta kasa fita a wan tu fayif sunanta Oriyo. Sannan  ita za a kaɗa wa Oriyo.

    Yayin da wata ta yi jirel, ko kuma aka samu musu, to za a kaɗa ojo. Ojo kaɗi uku ne da ake sake yi tare da waƙa ta daban. Wadda ta yi nasara za ta ce: “Ba ga shi ba!” Wato hakan na nuna da ma ita ke da gaskiya, ɗayar ce ta tayar da musun rashin gaskiya. Waƙar kaɗin ojo ita ce:

    Ojo,

    Ojollo-ojollo mama,

    Ojollo-ojollo mama,

    Mama ojollo.

    Wani lokaci kuma akan ce:

    Ojo,

    Ojo-ojo-ojo.

    6.18.3 Sakamakon Wasa

    Wadda ta kasa fita a wasan babunna to za a kaɗa mata oriyo. Wannan kuwa waƙa ce ta tsantsar tsokala ko zolaya da wadda ta faɗi ga babunna. Wannan ya haɗa da zungura da waƙar tsokala. Ga waƙar oriyo kamar haka:

    Mai Bayarwa: O oriyoriyo,

    Amshi: Oriyon gaye.

    Mai Bayarwa: Waye ya ce ta yi?

    Amshi: Oriyon gaye.

    Mai Bayarwa: Ko saurayinta ne,

    Amshi: Oriyon gaye.

    Mai Bayarwa: Shi ma ba zai yi ba.

    Amshi: Oriyon gaye.

    Mai Bayarwa: Ta sha ruwan fatari!

    Amshi: Oriyon gaye.

    Mai Bayarwa: Ku zuzzungure ta man ko kuna tsoronta ne?

    Amshi: Oriyo!

    Mai Bayarwa: Ta Allaji Ado ta yi kuɗi tana mana yangar.

    Amshi: Coriyo!

    Mai Bayarwa: Cara mara.

    Amshi: Cangwara ƙwai.

    Mai Bayarwa: A tottoshe kar ta haifi leda bak!

    Amshi: Oriyo!

    Mai Bayarwa: Riri-riri.

    Amshi: Oriyo!

    Haka za a yi ta mata wannan zolaya har sai ta yanka wata daga cikin ‘yan wasa. Za ta yi yankar ta hanyar sanya hannunta a wuyar ɗaya daga cikin ‘yan wasa sai a ja. Yayin da aka je yanka ‘yar wasa kuwa, to za ta yi gaggawar tsugunawa. Ba a yanka a tsugune, don haka dole Oriyo ta haƙura da yanka wadda ta tsuguna. Yayin da ta yanka wata kuwa, to wadda aka yanka ita ce Oriyo, kuma ita za a koma kaɗa wa Oriyo.

    6.18.4 Tsokaci

    Wannan wasa na buƙatar zurfafa tunani da karantar tunanin juna. Yayin kowane kaɗi, mai yi za ta riƙa faman saɓa wa da abokiyar yin ta, yayin da ita kuma za ta riƙa ƙoƙarin ƙwacewa. Sannan hanya ce ta motsa jini ga yara da ‘yanmata. Sakamakon wasan kuwa na sanya mai wasa ta dage wajen ba ta zama ta Oriyo ba.

    WASANNI A ƘASAR HAUSA

    Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.