A Fim-Fim-Fim

    6.19 A Fim-Fim-Fim

    Wannan wasa ne da za a iya hasashen ya samu ba da jimawa ba. Wato bai samu ba sai bayan boko ya yaÉ—u sosai a Æ™asar Hausa. Za a iya kallon hakan daga cikin irin kalaman Ingilishi da ake amfani da su yayin gudanar da wannan wasa.

    6.19.1 Wuri Da Lokacin Wasa

    Kasancewar wasan na zamani, an fi gudanar da shi a makarantu, musamman na sakandare da firamare. Sai dai akan gudanar da shi a dandali, musamman idan aka samu taron yaran da sun koye shi daga makaranta. Sannan akan yi wannan wasa a gidan biki.

    6.19.2 Yadda Ake Wasa

    Yara daga huÉ—u zuwa sama ne suke gudanar da wannan wasa. Yawansu zai iya kasancewa har goma ko ma sama da haka. Amma mutane huÉ—u ne suke yi a lokaci guda. A yayin da suke yi, sauran za su tsaya su zuba musu idanu. Yayin da É—aya ta faÉ—i, sai ta fita wata kuma ta maye gurbinta.

    Yara huÉ—u za su tsaya suna fuskantar juna daga kusurwoyi huÉ—u. Wato biyu suna fuskantar juna, haka ma ragowar biyun. Daga nan za su fara tafi da kuma waÆ™a kamar haka:

    Wan,

    Tu,

    Tiri,

    Fo.

    Daga nan kuma za su fara tafawa da juna cikin canza salo. Akan yi tafin ta gaba da ta gefen hagu da gefen dama. Yayin da ake wannan tafi, za a riÆ™a waÆ™a kamar haka:

    Ges-ges-ges,

    Tu zeiz,

    Tu ze west,

    Tu left an rayit,

    Gib mi dokto,

    Ba ni askirin ba ni firinta,

    A fim-fim-fim.

    Daga nan kuma za a fara lissafo abacada na Turanci har zuwa /z/. Yayin da ake yi, wadda ta faÉ—i za ta fita, yayin da ta gefenta za ta shigo a ci gaba.

    6.19.3 Tsokaci

    Wannan wasa hanya ce ta motsa jini tare da nishaÉ—i ga yara. Sannan wasa ne mai buÆ™atar nutsuwa, saboda haka, yana sanya nutsuwa ga yara.

    WASANNI A ƘASAR HAUSA

    Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.