Ticker

Kis-Kis-Kis An Kas-Kas-Kas

6.21 Kis-Kis-Kis An Kas-Kas-Kas

Wannan wasa ne mai kama da bena. Shi  ma wasa ne na dandali. Adadin yaran da ke gudanarwa na farawa daga biyu zuwa sama da haka.

6.21.1 Wuri Da Lokacin Wasa

i. An fi gudanar da wannan wasa a dandali.

ii. Akan gudanar da wannan wasa da hantsi ko da yamma, musamman da farkon damina.

6.21.2 Kayan Aiki

Ƙaramin dutse ko fashasshiyar kwalba ko makamantansu a matsayin ‘yar  jifa.

6.21.3 Yadda Ake Wasa

Akan yi amfani da guntun kara ko ƙaramin itace a zana gidan dara manya a ƙasa. Yakan kasance layuka uku a jere. An fi yin gidajen dara goma-goma a kowane layi. Adadin gidajen zai kasance talatin ke nan. Kowacce za ta zaɓi abokiyar wasanta, kasancewar wasan ta bibbiyu ake yi.

Masu wasa za su tsaya a gaban layuka. Daga nan za su yi waƙa kamar haka:

Kis-kis-kis an kas-kas-kas,

Wan bena,

Tu bena,

Tiri lamba.

Daga nan za su naɗe ƙafafu ɗaɗɗaya. Kowacce za ta shiga gidan farko da ke gefen da take. Daga nan za su riƙa tsalle a tare. Za su shiga gidan tsakiya tare, sai kuma kowacce ta koma gidan gefe amma na gaba da wurin da suka tsallako. Yayin da suka je ƙarshen gidajen, to za su juyo. Idan suka juyo suka kawo farkon layi, to za su sayi gida. Za su je su yi alama ta hanyar zane a gidan da suka saya. Daga nan babu mai hurmin shiga musu gida ba tare da izinin waɗanda suka sayi gidan ba. Waɗanda suka sayi gidaje sama da na saura, su ake kira ‘yan asali.

6.21.4 Wasu Dokokin Wasa

i. Yayin da ɗaya daga cikin masu wasa ta faɗi (‘yan gari ɗaya) to dukkanninsu sun faɗi.

ii. Masu wasa ba su da damar taka gidan da aka saya ba tare da izinin masu gidan ba.

6.21.5 Tsokaci

Wannan wasa hanya ce ta motsa jiki ga yara. Sannan yana koyar da ƙwarewar seti wajen jifa. Baya ga haka, wasan yana koyar da nutsuwa, kamar yadda rashin nutsuwa kan kai ga mai wasa ta faɗi cikin gaggawa. Wani abin burgewa ga wannan wasa shi ne yadda yara biyu ke abu iri guda a lokaci guda cikin ƙwarewa ba tare da saɓa wa tunanin juna ba.

WASANNI A ƘASAR HAUSA

Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


Post a Comment

0 Comments