Ladidin Baba

    6.23 Ladidin Baba

    Wannan ma wasa ne na dandali. Amma yanzu da makarantu suka yawaita, yara mata na yawan gudanar da wannan wasa a makarantu. Kimanin mutane ishirin zuwa sama ne suke gudanar da wannan wasa. Yawansu na iya kaiwa talatin ko sama da haka.

    6.23.1 Wuri Da Lokacin Wasa

    i. Asalin wasan na dandali ne, amma akan gudanar da shi a makarantu ko gidajen biki da aka samu taron yara mata.

    ii. An fi gudanar da wasan da dare, ko lokutan makaranta.

    6.23.2 Yadda Ake Wasa

    Yara sukan kasance a da’ira. Yara biyu kuma sukan kasance a tsakiya. Daga nan yaran da ke bisa da’ira za su fara tafiya suna zagaya waÉ—anda suke tsakiya, tare da tafi. ÆŠaya daga cikin waÉ—anda ke tsakiya kuma za ta riÆ™a nuna‘yaruwarta cikin zolaya, yayin da ake waÆ™a, tamkar dai waÆ™ar a kanta take magana. Yayin da aka gama waÆ™ar, to wadda ke nuni za ta fita ta koma cikin da’ira. Wata kuma za ta dawo tsakiya, inda É—ayar za ta riÆ™a nuna ta yayin da ake waÆ™a.

    6.23.3 WaÆ™ar Wasa

    Ladidin baba,

    Ta ci tuwonta da manta da yajinta,

    Wa zai wanke kwanon?

    Wanda ya raina ubansa É“arawo ne,

    Ga abin mamaki,

    ‘Yar akuya da wanke-wanke,

    Har da omon goma,

    Had da zama a kan kujera,

    Baba ka cuce ni,

    Tun da ka kai ni Kwantagora,

    Kwantagora gari ne,

    Amma ba garin zuwa ba,

    Daga mai shan taba,

    Sai mai shan giya da Æ™waya,

    Ƙarfi ya Æ™are sai an tokara da sanda.

    6.23.4 Tsokaci

    Wannan wasa hanya ce ta samar da nishaÉ—i da kuma motsa jiki ga yara. Sannan waÆ™ar da ke cikin wasan na hannunka-mai-sanda zuwa ga barin wasu halaye na Æ™i da suka haÉ—a da raina iyaye da kuma shaye-shaye irin na giya da Æ™waya.

    WASANNI A ƘASAR HAUSA

    Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.