Na Daura Kallabi

    6.24 Na ÆŠaura Kallabi

    Wannan ma wasan dandali ne na mata. Wannan wasan ma na buÆ™atar adadin yara da yawa. Dole yawansu ya kasance daga ishirin zuwa sama.

    6.24.1 Wuri Da Lokacin Wasa

    i. Asalin wasan na dandali ne, amma akan gudanar da shi a makarantu ko gidajen bikin da aka samu taron yara mata.

    ii. An fi gudanar da wasan da dare, ko lokutan makaranta.

    6.24.2 Kayan Aiki

    Kallabi/Kwali/ÆŠankwali

    6.24.3 Yadda Ake Wasa

    Yara sukan yi da’ira. Daga nan biyu daga cikinsu za su shiga tsakiya. ÆŠaya daga cikin waÉ—anda ke tsakiya za ta yi gwaggwaro ta cokara kallabinta a goshi. Daga nan wadda ta cokara kallabi za ta riÆ™a waÆ™a yayin da sauran kuma suke amsawa. Sannan waÉ—anda ke bisa da’irar za su riÆ™a zagayawa tare da tafi. WaÆ™ar ita ce kamar haka:

    Mai WaÆ™a: Na É—aura kallabi,

    Kallabin rashin kunya.

    ‘Yan Wasa: Alo.

    Mai WaÆ™a: Sai Sa’a ta ture min.

    ‘Yan Wasa: Alo.

    A wannan gaci, É—ayar da ke tsaye a tsakiya za ta ture kallabin da mai waÆ™ar ta cokara kanta. Daga nan kuma za a ci gaba da waÆ™a:

    Mai Waƙa: Ko ubanta wane ne.

    ‘Yan Wasa: Alo.

    Mai WaÆ™a: Ko ubanta sarki ne.

    ‘Yan Wasa: Alo.

    Mai WaÆ™a: Ba sarki ba ko Gwamna,

    ‘Yan Wasa: Alo.

    Mai WaÆ™a: Ba gwamna ba ko shugan Æ™asa,

    ‘Yan Amshi: Yaraye,

    Mai WaÆ™a: Da wa ne nake faÉ—i,

    ‘Yan Amshi: Yaraye,

    Mai WaÆ™a: Da Fatinake faÉ—i,

    Sai ta zo mu É—an girgiza kaÉ—an,

    Girgizar da ba kunya.

    ‘Yan Amshi: Alo.

    Daga nan za su É—an yi rawa ita da wadda ta ambaci sunanta. Yayin da suka Æ™are wannan rawa, to sai mai waÆ™a ta fita wata kuma ta shigo.

    6.24.4 Tsokaci

    Wannan wasa hanya ce ta samar da nishaÉ—i da raha da kuma motsa jiki ga yara mata.

    WASANNI A ƘASAR HAUSA

    Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.