Laula Amarya

    6.25 Laula Amarya 

    Wannan wasa ne da yara mata ke gudanarwa a lokacin bukukuwan aure. Kimanin yara goma zuwa sama ne suke gudanar da wannan wasa. Yawan nasu ya danganta da irin taron da aka yi a auren, wanda hakan na da alaÆ™a da yawan Æ™awaye da amaryar ke da su.

    6.25.1 Wuri Da LokacinWasa

    i. Ana gudar da wannan wasa ne a gidajen Bukukuwan aure. Sai dai ba a wuri É—aya ake tsayawa ba. Akan fara tun daga gidansu amarya yayin da za a kai ta É—akinta, har zuwa gidan mijin nata.

    ii. Akan gudanar da wannan wasa ne da dare ko dai duk wani lokacin da za a kai amarya É—akinta.

    6.25.2 Yadda Ake Wasa

    Yara mata (waÉ—anda yawanci Æ™awayen amarya ne) sukan taru yayin da za a raka amarya zuwa gidanta. Daga nan za su fara waÆ™a tare da tafi. Wata ko wasu daga cikin yaran za su riÆ™a ba da waÆ™a, saura kuwa suna amsawa tare da tafi. WaÆ™ar da ake yi ita ce:

    Bayarwa: Laula amarya,

    Amshi: Laula.

    Bayarwa: Bari kuka Æ™anuwata,

    Amshi: Laula.

    Bayarwa: Bari kuka yarinya,

    Amshi: Laula.

    Bayarwa: Ba aure zan miki ba,

    Amshi: Laula.

    Bayarwa: Makaranta zan kai ki,

    Amshi: Laula.

    Bayarwa: Makarantar masu gari.

    Amshi: Laula.

    6.25.3 Tsokaci

    Wannan waÆ™a na samar da nishaÉ—i da annashuwa ga yara. Bayan haka, waÆ™ar na É—auke da wani saÆ™o na faÉ—akarwa ga amarya, cewa aure makaranta ce. Sannan tana ba da haÆ™uri da kwantar wa amarya hankali.

    WASANNI A ƘASAR HAUSA

    Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.