Barawo Me Ka Sata?

    6.26 Ɓarawo Me Ka Sata?

    Wannan ma wasan dandali ne. Wannan wasa ma na buƙatar jama’a da dama yayin gudanar da shi. Yawansu na iya kaiwa ishirin ko sama da haka.

    6.26.1 Wuri Da LokacinWasa

    i. Asalin wasan na dandali ne, amma akan gudanar da shi a makaranta ko gidajen bikin da aka samu taron yara mata.

    ii. An fi gudanar da wasan da dare, ko lokutan makaranta.

    6.26.2 Yadda Ake Wasa

    Yara sukan yi da’ira. Daga nan mutane biyu sukan shigo tsakiya. Ɗaya za ta riƙa tambayar ɗaya, yayin da ɗayar za ta riƙa ba ta amsa. Sauran yara za su riƙa bin bakin mai amsawa. Wato su riƙa faɗin amsar tare kamar haka:

    Tambaya: Ɓarawo me ka sata?

    Amsa: Ƙaya.

    Tambaya: Mudu nawa ne?

    Amsa: Biyu.

    Tambaya: Faɗi gaskiyarka.

    Amsa: Uku.

    Tambaya: Me sunanka?

    Amsa: Musa Sale hancin Asabe.

    Tambaya: Ina gidanku?

    Amsa: Gidan da ake ta soye-soye,

    A soya nama,

    A soya fuka-fukin agwagwa.

    Tambaya: Zaɓi naka.

    Daga lokacin da aka faɗi haka dukkanin yaran da ke bisa da’ira za su miƙo hannu. Mai waƙa kuma za ta zaɓi ɗaya daga cikinsu ta hanyar ɗora hannunta bisa nata. Sannan za su yi rawa da girgiza tare da waƙa kamar haka:

    Cin-cin o,

    Cilla ƙashin-ƙashin ɗaya,

    Cilla ƙashin-ƙashin biyu.

    6.26.3 Tsokaci

    Wannan wasa hanya ce ta motsa jiki ga yara. Sannan yana samar da annushuwa da raha tsakanin masu gudanarwa da kuma masu kallo.

    WASANNI A ƘASAR HAUSA

    Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.