Rana Ta Fito Gabas

    6.28 Rana Ta Fito Gabas

    Wannan ma wasan gaÉ—a ne na dandali. Kimanin yara goma zuwa sama da haka ne suke gudanar da wannan wasa.

    6.28.1 Wuri Da Lokacin Wasa

    i. Asalin wasan na dandali ne, amma akan gudanar da shi a makarantu ko gidajen bikin da aka samu taron yara mata.

    ii. An fi gudanar da wasan da dare, ko lokutan makaranta.

    6.28.2 Yadda Ake Wasa

    Yara za su yi da’ira, yayin da É—aya daga cikinsu za ta shiga tsakiya. Wadda ke tsakiyar za ta riÆ™a ba da waÆ™a, yayin da sauran kuma ke amsawa tare da tafi. Yayin da suka Æ™are, sai yarinyar da ke tsakiya ta koma cikin da’ira. Wata kuma za ta fito domin ci gaba da wasa.

    6.28.3 WaÆ™ar Wasa

    Mai Bayarwa: Rana ta fito gabas,

    ‘Yan Amshi: Ta faÉ—a a yamma.

    Mai Bayarwa: Ga wani malami ya fito,

    ‘Yan Amshi: Da baÆ™ar takarda.

    Mai Bayarwa: Shi ma malamin ba shi kunya,

    Yan Amshi: Ba shi tsoro.

    Mai Bayarwa: Iya,

    ‘Yan Amshi: Iya ga rawa-rawa ga rawa.

    Mai Bayarwa: Iya ga rawar,

    ‘Yan Amshi: Kurege.

    Mai Bayarwa: Yaro ba zai iya ba,

    ‘Yan Amshi: Ni ma da Æ™yar na koya.

    Mai Bayarwa: Da gudu da tsalle-tsalle,

    ‘Yan Amshi: Da fuka-fukin agwagwa.

    Daga nan za a haÉ—a baki da mai bayarwa da masu amshi kamar haka:

    Gwana-gwana,

    Gwana ta kaÉ—a zare,

    Ta ce gwani zo ka saya,

    Sule talatin da biyar,

    In ba biyar ba ciniki.

    Mai kare kama karenka na ji kukan kura,

    A ina?

    A can tashar Gwangola,

    Inda mata ke haihuwa maza na yaye.

    Sharɓale-sharɓale,

    Mai rigar zinare,

    Alhajin da bai je haji ba,

    Ya kama jaka ya É—ira,

    Ya kai ta kantin sukari,

    Can sukari can sukari tsurut?

    6.28.4 Tsokaci

    Wannan wasa hanya ce ta motsa jiki ga yara. Sannan yana samar da raha da annushuwa ga masu yi da kuma masu kallo. Yaya aka yi suka koyi rawar kurege ta hanyar amfani da fuka-fukin agwagwa?

    WASANNI A ƘASAR HAUSA

    Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.