6.3 Allah Koro Ruwa - Daga Littafin WAƘOƘIN HAUSA NA GARGAJIYA (Page - 135)

    Citation: Gobir, Y.A. & Sani, A-U. (2021). Waƙoƙin Hausa Na Gargajiya. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-0-01.

    6.3 Allah Koro Ruwa

    Wannan waƙa tana da zubi da tsari iri guda na waƙar Caccayya. Abin da ya bambanta su kawai shi ne, kowace na ɗauke da waƙa mabambanciya da ta ‘yar uwarta. Waƙar Allah Koro Ruwa gajeruwa ce, kwata-kwata ba ta wuce ɗangwaye biyu ba. Ga yadda waƙar take:

    Allah koro ruwa na koma rafi,

    Ba na tsoron likita barai ɗan sanda.

    Haka za a yi ta maimaita wannan waƙa. Wannan waƙa tana samar da nishaɗi ga yara. Sannan tana ɗauke da addu’ar samun ruwan sama. Bayan haka kuma, akwai wani kurman baƙi da waƙar ta ƙunsa. Wannan kuwa shi ne faɗakarwa game da illoli da ke tattare da amfani da gurɓataccen ruwan rafi. Ko dai ta hanyar ɗiba a sha, ko wanka ko wani abu makamancin wannan. Shi ne yaran ke nuna cewa ba sa tsoron likita. ke nan ba sa tsoron wata cuta da za ta kama su daga cikin ruwan. Bayan haka, ba sa tsoron ɗan sanda. ke nan duk togaciyar da hukuma ke yi ba sa tsoron sa.

    WAƘOƘIN HAUSA NA GARGAJIYA

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.