O Aliyo

    6.30 O Aliyo

    Wannan ma wasan gaÉ—a ne da ‘yanmata ke gudanarwa a dandali. Mutane da dama ne ke haÉ—uwa domin gudanar da wannan wasan. Yawansu kan kai ishirin ko ma sama da haka.

    6.30.1 Wuri Da Lokacin Wasa

    i. Asalin wasan na dandali ne, amma akan gudanar da shi a makarantu ko gidajen biki da aka samu taron yara mata.

    ii. An fi gudanar da wasan da dare, ko lokutan makaranta.

    6.30.2 Kayan Aiki

    Kallabi /ÆŠankwali

    6.30.3 Yadda Ake Wasa

    Masu wasa sukan yi da’ira. Mutane biyu za su shiga tsakiya. Wasan yana tafiya da waÆ™a tare da tafi. Yayin da ake waÆ™ar, waÉ—anda ke kan da’ira za su riÆ™a zagawa tare da tafi. WaÆ™ar ita ce kamar haka: 

    Bayarwa: O Aliyo,

    O Aliyo,

    O Aliyo.

    Amshi: ’Yan mata.

    Bayarwa: Ina mijinki ne?

    Amshi: ‘Yan mata.

    Aliyar Gwangola: Ya yi tafiya.

    Amshi: ‘Yan mata.

    Bayarwa: Tun watan nawa?

    Amshi: ‘Yan mata.

    Aliyar Gwangola: Tun watan bakwai.

    Amshi: ‘Yanmata.

    Bayarwa: Za ki bi shi ne?

    Koko ba za ki bi shi ba?

    Amshi: ‘Yanmata.

    Aliyar Gwangola: Zan bi shi man.

    Amshi: ‘Yanmata.

    Bayarwa: Bi shi bi shi bi shi,

    Bi shi mana,

    Aliyar Gwangola.

    Daga nan Aliyar Gwangola za ta fara tafiya a hankali, wato dai tana bin mijinta. WaÆ™a kuma za ta ci gaba:

    Bayarwa: Haba dawo dawo dawo,

    Dawo mana,

    Amshi: Aliyar Gwangola.

    A wannan gaÉ“a Aliyar Gwangola za ta riÆ™a dawowa da baya da baya.

    Bayarwa: Haba mai da É—ankwali gindin goshi mana,

    Amshi: Aliyar Gwangola

    A wannan gaÉ“a Aliyar Gwangola za ta mayar da É—ankwalinta gaban goshi.

    Bayarwa: HaÉ“a É—ebo shoki ki ba su kunya,

    Amshi: Hasana a leda.

    A wannan gaÉ“a dukkanin ‘yan wasa za su tsuguna Æ™asa su yi wata ‘yar rawa da ake yi wa laÆ™abi da shoki. WaÆ™a kuma za ta ci gaba:

    Bayarwa: Sosa abinki babu kunya,

    Amshi: Hasana a leda.

    Da an kawo wannan gaÉ“a to za ta fita, sai wata kuma ta shiga.

    6.30.4 Tsokaci

    Wannan wasa hanya ce ta motsa jiki ga yara. Sannan yana É—auke da wani saÆ™o ga ma’aurata musamman ta hanyar nuna rashin dacewar miji ya bar matarsa na tsawon lokaci ba tare da ya waiwaice ta ba.

    WASANNI A ƘASAR HAUSA

    Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.