Tafa-Tafa

    6.31 Tafa-Tafa

    Wannan wasa ne na yara mata. Yara biyu maza su iya gudanar da wasan a tsakaninsu. Sai dai wani lokaci akan yi shi tsakanin yaran da suka kai shida, ko ma sama da haka.

    6.31.1 Wuri Da Lokacin Wasa

    i. Akan gudanar da wannan wasa a dandali ko wurin jaura ko wani wuri da yara ke haÉ—uwa.

    ii. Idan a dandali ake wannan wasa, yakan kasance da dare ne. Amma wani lokaci akan yi shi da hantsi ko da yamma, musamman a wurin jaura da ke tara hara da dama. A irin wannan lokaci, waÉ—anda suka sayar da kayan jaura za su iya wasanni daban-daban musamman yayin da suke jiran abokan tafiyarsu su Æ™arasa sayarwa.

    6.31.2 Yadda Ake Wasa

    Yara sukan tsaya su fuskanci juna. Daga nan za su fara tafa hannuwansu cikin salo daban-daban. Sukan tafa hannuwan dama, sannan su yi tafi (kowa ta tafa da kanta, wato ta haÉ—a hannuwanta na dama da na hagu). Sai kuma su tafa da hannuwan hagu, su kuma sake yin tafi. Sukan yi haka cikin Æ™warewa da gwaninta kuma cikin gaggawa. Yayin da suke wannan wasa, sukan yi waÆ™a kamar haka:

    Tafa-tafa,

    Tafiyar nan da za mu gobe,

    Da wa za mu yin ta?

    Daga Allah sai Ma’aiki,

    Sai É—an yaro masoyi,

    Ya masoyi jira ni,

    In daka in kirɓa,

    Kada kura ta ci mu tare,

    Idan ta ci mu tare,

    Allah ne gwanin iyawa,

    Annabi ne gwanin iyawa,

    Ke kaza da tone-tone,

    Kada ki tono wa kanmu,

    Abin duniya da rana tsaka fafal,

    ÆŠan mai dogon wuya zalam,

    HaÆ™oransa da gari buÉ—u.

    Yayin da aka saÉ“a wurin tafa hannu, to an É“ata a wasa ke nan. Saboda haka za a sako wasan daga fari. An samu wata waÆ™ar ta daban da ake amfani da ita yayin wasan a Æ™asar Katsina. Ta kasance kamar haka:

    Muna tafa-tafa,

    Akwai wanda nake so,

    Amma kunya na so,

    Ta wanke ni da soso,

    In faÉ—a ku ji kar ku yi dariya,

    Fari ne siriri,

    Yana da tsawo ga gashi,

    Ya iya kwalliya kamar É—an sarki,

    Na mori saurayi mai kyawu,

    Allah Ya sa yana da halin kirki

    Mu tafi mu ji daÉ—in zama,

    Mu yi wasa mu yi dariya.

    6.31.3 Tsokaci

    Wannan wasa yana samar da nishaÉ—i ga yara. WaÆ™ar wasan na É—auke da saÆ™on da ke nuni da cewa, duk abin da ya samu mutum to daga Allah ne. Wato dai tana koyar da imani da kuma tauhidi. WaÆ™ar ta biyu kuwa, tana bayyana Æ™udurin zuciya ta yaran da ke wasan.

    WASANNI A ƘASAR HAUSA

    Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.