6.3.3 Ilmantarwa/Karantarwa

     Citation: BunguÉ—u, U.H. (2021). Bara da wasu waÆ™oÆ™in bara a Æ™asar HausaAhmadu Bello University Press Limited.

    Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

    Dr. Haruna Umar BunguÉ—u
    (Sarkin Gobir Na BunguÉ—u)
    Email: harunaumarbungudu@gmail.com
    Phone: 08065429369

    Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar Hausa

    6.3.3 Ilmantarwa/Karantarwa

    Wani Jigo da ake samu a cikin waÆ™oÆ™in bara shi ne ilmantarwa. Ilmantarwa a nan yana nufin karantarwa. Jigon ilmantarwa shi ne wanda ke Æ™unsar ilmin yadda ake aiwatar da wata ibada a cikinsa. Irin wannan jigo a cikin waÆ™oÆ™in bara kamar kumbo kamar kayanta ne. Wato babu wani bayani na ilmi sosai a cikinsa, da yake masu tsara waÆ™oÆ™in su rera su ba masu cikakken ilmi ba ne. Da yawansu Almajirai ne ko Gardawa ko sauran mabrata kamar makahi da masu wata naÆ™asa. Suna tsara waÆ™oÆ™in ne domin jawo hankalin masu ba su sadaka a maimakon su je masu hannu rabbana, don haka É—an ilmin da ake ambato a ciki bai taka kara ya karya ba. Manufar samun wannan jigo a cikin waÆ™oÆ™in shi ne waÉ—anda ake yi wa bara musamman marasa ilmi daga ciki su ji kamar mai rera waÆ™ar malami ne saboda girman da ilmi yake da shi. Misalin wannan shi ne waÆ™ar “LaÆ™ada Raliyallahu” wadda a ciki ake cewa:

    Jagora: Laƙada raliyallahu anal muminina.

     Amshi: To.

    Jagora: Angal lahu angaruhin mu’asha.

     Amshi: To.

     Jagora: Inna in sallah ki kai ki É—auro da niyya,

     Amshi: To,

    Jagora: In Azumi ki kai ki É—auro da niyya,

    Amshi: To,

    Jagora: In zakka ki kai ki É—auro da niyya,

    Amshi: To,

    Jagora: In tsalki ki kai ki É—auro da niyya,

    Amshi: To,

    (Laƙad Raliyal Lahu)

    A cikin wannan waƙar mai barar na ilmantar da wadda yake yi wa bara muhimmancin niyya ga kowane aiki na ibada. Sai dai kamar yadda aka faɗa can baya masu waƙar ba malamai ba ne, don haka ɗan abin da za su faɗa ƙalilan ne. A waƙar da ta gabata tun daga layi na uku har zuwa ƙarshe ana sanar da mai saurare matsayin niyya a cikin aiki. Kusan ana sanar da shi cewa niyya ita ce ƙashin bayan kowane aiki na ibada. Wannan shi ya sa aka ambaci shikashikan Musulunci daga cikin biyar kuma kowane aka jaddada yin niya wajen yin sa. Aka fara ambaton sallah tare da jawo hankalin wadda ake yi wa bara cewa ta fara ɗaura niya idan za ta yi. Haka sauran ibadu na azumi da zakka. Daga ƙarshe a ɗa na huɗu wanda shi ya kamata a fara ambata, wato tsarkin zuciya wanda shi ne imanin da ayyukan suka rataya gare shi. Babu shakka ɗiyan waƙar da suka gabata ko ba su yi bayani mai yawa ba sun sanar da mai sauraro cewa aiki ba ya inganta sai da niya.

    Da yake mabarata da yawa ba masu ilmi ba ne, ya sa waÆ™oÆ™insu na ilmantarwa ba su da yawa. Ƙila shawar wannan jigo ya kai su ga aron rubutattun waÆ™oÆ™in ilmantarwa masu yawa suna bara da su. Kamar yadda aka ambata baya, rubutattun waÆ™oÆ™i an nazarin jigoginsu a matakan bincike dabam-daban, amma an kawo wani misali daga “WaÆ™ar Kiran Sallah” wadda take rubutatta ce kuma mabarata da yawa na amfani da ita wajen yin bara domin misali kawai ba domin wani sabon nazari ba.

    Allahu akbar in kiran sallah kakai,

    Don kak ka ce ala ka faÉ—i ga banza.

    Wannan alifi É—amre kablasan shikai

    Ak, kak ka ce akabar a bar ka ga banza.

    Akubar da akibar wanga dud dulginku na,

    Juhala’u kau da ka buÉ—e baki banza.

    Kuma ba a cewa bar batun akbar akai,

    Don kakka tashi ka buÉ—e baki banza.

     (Barmo Kwasare:WaÆ™ar Kiran Sallah)

    A waÆ™ar marubucin yana ilmantar da jama’a ne a kan yadda ake yin kiran sallah. Dubi yadda yake bayani a baiti na farko da na uku har ma da sauran baitocin.


    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.