Ina Da Cikin Dan Fari

    6.34 Ina Da Cikin Ɗan Fari

    Wannan wasa yana da zubi da tsari irin na wasan tafa-tafa. Abin da ya raba su kawai shi ne waƙoƙin da ake yi a ciki mabambanta ne. Sannan a waƙar wasan ina da cikin ɗan fari akwai amshi. A waƙar tafa-tafa kuwa babu amshi. Waƙar da ake yi cikin wasan ina da cikin ɗan fari ita ce:

    Bayarwa: Ina da cikin ɗan fari,

    Amshi: To!

    Bayarwa: Wata ɗaya ba wasa ba,

    Amshi: To!

    Bayarwa: Wata biyu ba wasa ba,

    Amshi: To!

    Bayarwa: Wata uku ba wasa ba,

    Amshi: To!

    Bayarwa: Wata huɗu ba wasa ba,

    Amshi: To!

    Bayarwa: Wata biyar ba wasa ba,

    Amshi: To!

    Bayarwa: Wata shida ba wasa ba,

    Amshi: To!

    Bayarwa: Wata bakwai ba wasa ba,

    Amshi: To!

    Bayarwa: Wata takwas ba wasa ba,

    Amshi: To!

    Bayarwa: Sai a ran na goma na goma,

    Amshi: To!

    Bayarwa: Na haifi ɗana Mamman,

    Amshi: To!

    Bayarwa: Na je gidanmu da wanka,

    Amshi: To!

    Bayarwa: Na tarad da baba a zaure,

    Amshi: To!

    Bayarwa: Yana cikin cinikinsa,

    Amshi: To!

    Bayarwa: Yana cinikin goronsa,

    Amshi: To!

    Bayarwa: Yace mu ga jikan namu,

    Amshi: To!

    Bayarwa: Jikan namu har ya girma?

    Amshi: To!

    Bayarwa: Ya tsunkule shi a hanci,

    Amshi: To!

    Bayarwa: Na ce uhm! Ba komai,

    Amshi: To!

    Bayarwa: Ya ce ku ji ɗiya ba kunya?

    Amshi: To!

    Bayarwa: Ya ce ku ji ɗiya ‘yar banza!

    Amshi: To!

    6.34.1 Tsokaci

    Waƙar wannan wasa tana ɗauke da hoton ciki da haihuwa. Wato kamar yadda sai ciki ya kai watanni, (tara a mafi yawan lokuta) kafin a haife shi. Sannan waƙar madubi ce da ke hasko al’adar Bahaushe ta kunyar ɗan fari.

    WASANNI A ƘASAR HAUSA

    Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.