Gamuna

    6.40 Gamuna 

    Wannan wasan dandali ne na mata. Ana buÆ™atar yara da dama domin gudanar da wannan wasa. Saboda haka, yawan masu gudanarwar na kasancewa ashirin zuwa sama a mafi yawan lokuta.

    6.40.1 Wuri Da Lokacin Wasa

    i. Akan gudanar da wannan wasa a dandali ko gidan biki ko wani wuri da ake samun taron yara mata.

    ii. Akan gudanar da wannan wasa da hantsi ko da yamma ko kuma da dare, lokacin farin wata.

    3.40.2 Yadda Ake Wasa

    Masu wasa za su rabu zuwa gari biyu. Za a yi Æ™oÆ™arin daidaita yawan ‘yan garuruwan guda biyu. ‘yan gari É—aya daga cikin garuruwan biyu za su tsuguna su dafa kafaÉ—un juna. ‘Yan É—aya garin kuma za su koma can gefe, su ba su tazara. Daga nan za su tattauna tsakaninsu kan wadda za su É—auka daga garin waÉ—anda suka tsuguna. Da zarar sun Æ™are tattaunawa sai su dawo. Za su zo daf da waÉ—anda ke tsugune, yayin da suke dafe da kafaÉ—un juna. Yayin da suka zo, za su fara waÆ™a wanda a wannan lokaci ne kuma garin da ke tsugune za su tashi su riÆ™a ba su amsa. Haka za su riÆ™a yi suna rangaji tare da ‘yan taku zuwa gaba da baya. WaÆ™ar ita ce kamar haka:

    Masu ÆŠauka: Ga mu nan muna zuwa,

    Muna zuwa muna zuwa,

    A cikin JSS Misau.

    Masu Bayarwa: Meye dalilin zuwanku?

    Zuwanku zuwanku,

    A cikin JSS Misau?

     

    Masu ÆŠauka: Za mu É—auki É—ayarku,

    ÆŠayarku É—ayarku,

    A cikin JSS Misau.

    Masu Bayarwa: Da sai ku faÉ—a mana sunanta,

    Sunanta sunanta,

    A cikin JSS Misau.

     

    Masu ÆŠauka: Da za mu É—auki A’isha,

    A’isha A’isha,

    A cikin JSS Misau.

    A wannan gaÉ“a za su kama wadda suka ambaci sunanta sannan su dawo da ita cikinsu. Daga nan kuma za su fara tsalle tare da faÉ—in:

    Mu gidanmu ba yunwa,

    Sai biredi sai shayi,

    Sai abincinTurwa,

    Abin da muke ci ba kwa ci.

    Daga nan za su koma can nesa kaÉ—an su tsuguna. Garin da aka É—auke musu ‘yar wasa kuma za su tattauna game da wadda za su É—auko. Haka za a ci gaba da wasa har sai an gaji.

    6.40.3 Tsokaci

    Wannan wasa ne na nishaÉ—i tsakanin yara. Sannan hanya ce ta motsa jiki gare su.

    WASANNI A ƘASAR HAUSA

    Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.