Dinga-Dinga

    6.46 Dinga-Dinga

    Wannan ma wasa ne daga cikin wasannin tashe na mata. Kimanin mutane biyar zuwa sama ne suke gudanar da wannan wasa. Kamar sauran wasannin tashen mata, an fi gudanarwa da dare, bayan an sha ruwa; wato cikin watan azumi. Sannan akan bi gida-gida ne domin gudanar da tashen.

    6.46.1 Kayan Aiki

    Kayan mata tsoffi kuma marasa kyau. Misali:

    i. Takalma

    ii. Zane

    iii. Riga

    iv. Mayafi

    v. Kallabi

    6.46.2 Yadda Ake Wasa

    ÆŠaya daga cikin yara za ta yi shiga mara kyau ta hanyar sanya kayayyakin da aka lissafo a Æ™arÆ™ashin 6.46.1. Za ta shige gaba sauran yara kuma na biye da ita. Yayin da suke cikin gida domin tashe, wannan yarinya za ta riÆ™a taku É—aiÉ—ai. A cikin sauran yara kuwa, É—aya za ta riÆ™a ba da waÆ™a yayin da saura ke amsawa. Ga waÆ™ar kamar haka:

    Bayarwa: Dinga-dingar gaye,

    Amshi: Shegiyar ‘yar banza!

     

    Bayarwa: Uwarta ba ta son ta,

    Amshi: Shegiyar ‘yar banza!

     

    Bayarwa: Ubanta ba ya son ta,

    Amshi: Shegiyar ‘yar banza!

     

    Bayarwa: Saboda kayan salla,

    Amshi: Shegiyar ‘yar banza!

     

    Bayarwa: Ba ta da kayan salla,

    Amshi: Shegiyar ‘yar banza!

     

    Bayarwa: Ba ta da rigar salla,

    Amshi: Shegiyar ‘yar banza!

     

    Bayarwa: Ba ta da zanen salla,

    Amshi: Shegiyar ‘yar banza!

     

    Bayarwa: Ba ta takalmin salla,

    Amshi: Shegiyar ‘yar banza!

     

    Bayarwa: A ba ta ko É—an sisi,

    Amshi: Shegiyar ‘yar banza!

     

    Bayarwa: Ta samu kayan salla,

    Amshi: Shegiyar ‘yar banza!

     

    Bayarwa: Dinga-dingar gaye,

    Amshi: Shegiyar ‘yar banza!

    Haka za su ci gaba da wannan waÆ™a yayin da Dinga kuwa ke ta faman zazzagawa da tsummokaran kaya jikinta. Wato dai ga salla ta zo amma saboda iyayenta sun Æ™i ta, ba ta da kayan salla.

    6.46.3 Tsokaci

    Wannan wasa na samar da nishaÉ—i ga masu yi da kuma musamman masu kallo. HaÆ™iÆ™a bara ne cikin wayo. Dole ne a ji tausayin kasancewar Dinga ba ta da kayan salla, ga kuwa salla ta zo. Don haka sisin da aka roÆ™a a ba wa Dinga saboda ta samu kayan salla ba zai gagara ba.

    WASANNI A ƘASAR HAUSA

    Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.