Ni Madara Ni Zuma

    6.50 Ni Madara Ni Zuma

    Wannan wani wasa ne da bai fiye tsawo ba. Wato akan ɗan yi shi ne kawai na ƙanƙanin lokaci ko dai kafin a fara wasa ko kuma bayan an kamala wani wasa kafin a sauya wani. Wani lokaci kuma akan yi shi ne bayan an tashi a wasa. Mutane uku zuwa sama ne suke gudanar da wannan wasan. Sannan ba ya buƙatar kayan aiki.

    6.50.1 Wuri Da LokacinWasa

    i. Wannan wasa ba ya da takamaiman wurin gudanar da shi. Domin kusan ba ya dogaro da kansa, sai ya haɗu da wani wasa na daban, kamar dai yadda aka yi bayani a sama. Saboda haka, ana yin wasan cikin gida ko dandali ko wurin sauran yara.

    ii. Akan yi shi da hantsi ko da yamma ko ma da dare.

    6.50.2 Yadda Ake Wasa

    Yayin da ake tsaye ko zaune, ɗaya daga cikin yara za ta tsiro da wannan wasa. Za ta yi haka ne ta hanyar fara waƙar wasan. Daga nan sai wasu yaran su amsa mata. Haka za a ɗan yi wannan wasa na lokaci ƙanƙani kafin a ci gaba da ainihin wasan da ake son yi. Waƙar wasan kuwa ita ce:

    Yarinyar Farko: Ni madara

    Yarinya Ta Biyu: Ni zuma

    Yarinya Ta Uku: Ni alkakin zuma

    Wani lokaci akan yi wannan waƙa ne yayin da ake bisa hanyar wasa. Misali idan aka ce: “Ku zo mu je mu yi wasan carafke.” Sauran yara kuma suka amince da haka; to za a iya wannan wasa yayin da aka ɗunguma zuwa wurin da za a zauna.

    6.50.3 Tsokaci

    Wannan wasa ya kasance tamkar mabuɗi ko marufi ga wasanni; ko kuma mahaɗi a wasu lokuta. Yana mazaunin mabuɗi idan aka buɗe fagen wasanni da shi. Yakan kasance marufi ko makulli kuwa, yayin da ya kasance wasan da aka gudanar yayin watsewa daga filin wasa. Za kuma ya kasance mahaɗi yayin da aka gudanar da shi bayan wani wasa kafin a fara wani. Waƙar da ke cikin wasan na nuna danƙon zumunci da ke tsakanin yara. Wato tamkar yadda zuma da madara da kuma alkakin zuma suke; yayin da aka tarar da alkaki, to za a tarar da madara da zumar.

    WASANNI A ƘASAR HAUSA

    Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.