6.51 Ni Mota Nake So
Wannan ma wasan gaɗa ne da ke da buƙatar yara da yawa domin gudanarwa. Adadin masu gudanarwar na iya kaiwa ishirin ko sama da haka. Ba a buƙatar wani kayan aiki domin gudanar da shi. Sannan yana cikin rukunnen wasannin gaɗa masu tafiya da waƙa.
6.51.1 Wuri Da Lokacin Wasa
Kasancewar wasan na gaɗa, an fi gudanar da shi a dandali da dare, musamman lokacin farin wata.
6.51.2 Yadda Ake Wasa
Yara sukan yi da’ira mai ɗan faɗi. Wato za su riƙa ba da ‘yar tazara tsakanin juna. Daga nan sai guda ɗaya ta fito tsakiya. Za ta riƙa ba da waƙa sauran kuma na amsawa. Ga yadda waƙar take:
Bayarwa: Ni mota nake so,
Amshi: Yayin mota ya wuce ki da aure.
Bayarwa: Ni mashin nake so,
Amshi: Yayin mashin ya wuce ki da aure.
Bayarwa: Ni keke nake so,
Amshi: Yayin keke ya wuce ki da aure.
Bayarwa: Ni jirgi nake so,
Amshi: Yayin jirgi ya wuce ki da aure.
Bayarwa: Ni allura nake so,
Amshi: Je ki gidan Malam Nagajere,
Ya iya allura talatin,
Wanda Bature bai iya ba,
Jish kankana jish kankana.
Jish kankana jish kankana.
Daga nan dukkanin masu wasa za su ɗan taka rawa. Da zarar sun ƙare, to wannan za ta koma cikin da’ira. Wata daban kuma za ta fito domin ci gaba da wasa.
6.51.3 Tsokaci
Wannan wasa hanya ce ta samar da nishaɗi da kuma motsa jiki ga yara. Waƙar wasan na ɗauke da wani saƙo da ya shafi burin ‘ya’ya mata yayin aure.
Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.