6.53 Ayye Rashidalle
Wannan wasan mata ne mai tafiya da waƙa, Sai dai ba ya buƙatar kayan aiki domin gudanar da shi. Kimanin yara huɗu ne zuwa sama suke gudanar da wannan wasa.
6.53.1 Wuri Da Lokacin Wasa
i. Akan gudanar da wannan wasa a dandali ko a gida. Sannan bayan samuwa da yawaitar makarantun boko, akan gudanar da wannan wasa a irin waɗannan makarantu.
ii. Ana gudanar da wannan wasa da hantsi ko da yamma ko da dare, musamman lokacin farin wata.
6.53.2 Yadda Ake Wasa
Yara sukan jeru, manne jikin juna. Ɗaya daga cikinsu kuma za ta kasance a gaba. Za ta riƙa faɗowa jikinsu, su kuwa za su riƙa cafe ta ba tare da sun bar ta ta kai ƙasa ba. Da sun cafe ta kuwa, za su cilla ta gaba. Babu wani suna na musamman da wasan ya ware wa waɗanda suke jeren da kuma wadda ke gaba. Amma saboda fayyacewa, wannan Littafi ya ba ta suna mai direwa, sauran yaran kuwa, masu cilli. Yayin da suke wannan wasa, mai direwa za ta riƙa ba da waƙa, saura kuwa na mata amshi. Ga yadda abin yake:
Mai Direwa: Ayye Ra,
Masu Cilli: Ayye Rashidalle.
Mai Direwa: Rashida mai koko,
Masu Cilli: Rashidalle.
Mai Direwa: Wadda ba ta wanka.
Masu Cilli: Rashidalle.
Mai Direwa: Wadda ba ta wanki,
Masu Cilli: Rashidalle.
Mai Direwa: Sai ruwan sama ya zo,
Masu Cilli: Rashidalle.
Mai Direwa: Sai ka gan ta a gona,
Masu Cilli: Rashidalle.
Mai Direwa: Tana roro-roro,
Masu Cilli: Rashidalle.
Mai Direwa: Tana roron wake,
Masu Cilli: Rashidalle.
Mai Direwa: Ayye Ra Ayye Rashidalle
Masu Cilli: Ayye Rashidalle.
6.53.3 Tsokaci
Wannan wasa yana samar da nishaɗi ga yara. Sannan hanya ce ta motsa jiki gare su. Waƙar wasan kuwa ta taɓo ƙazamai. Tana nuni da cewa, ba gwaninta ba ne mutum ya duƙufa ga aiki kawai, da har zai rasa lokacin tsafta.
Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.