Ayye Mama

    6.56 Ayye Mama

    Wannan na ɗaya daga cikin wasannin yara mata da suke gudanarwa yayin kai amarya. Yana cikin rukunin wasanni da ke tafiya da waƙa. Kasancewar a al’adar Bahaushe akan kai amarya ne ɗakinta da dare, za a iya cewa da dare ake gudanar da wannan wasa. Adadin masu gudanarwar kuwa ya danganta da yawan ƙawayen amarya.

    6.56.1 Yadda Ake Wasa

    Yayin da aka ɗunguma zuwa gidan amarya. Ɗaya daga cikin abokan amaryar za ta sanya waƙa. Saura kuwa za su riƙa amsawa tare da tafi. Ga yadda waƙar take:

    Bayarwa: Ayye mama ayye mama,

    Amshi: Mamaye iye.

    Bayarwa: Ayye mama labo-labo,

    Amshi: Mamaye iye.

    Bayarwa: Ayye Halima kin tafiyarki?

    Amshi: Mamaye iye.

    Bayarwa: Don haka kin shige ɗakinki?

    Amshi: Mamaye iye.

    Bayarwa: Ayye mama labo-labo,

    Amshi: Mamaye iye.

    Bayarwa: An ce Halima mun rabu ke nan?

    Amshi: Mamaye iye.

    Bayarwa: Ayye mama labo-labo,

    Amshi: Mamaye iye.

    Haka za a ci gaba da yi har sai an isa ɗakin amarya ko kuma an canza wata waƙa daban.

    6.56.2 Tsokaci

    Wannan wasa yana samar da nishaɗi ga masu raka amarya. Duk nisan wuri kafin a farga za a ga har an iso saboda shagaltuwa da aka yi da waƙe-waƙe. Waƙar wasan kuma tana ɗauke da saƙon bankwana zuwa ga amarya.

    WASANNI A ƘASAR HAUSA

    Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.