Ticker

Kada

Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.

6.60 Kaɗa

Wannan wasan yara mata ne da ke tafiya da waƙa. Ba ya buƙatar kayan aiki domin gudanarwa. Yawanci kimanin yara sama da goma ne suke gudanar da shi.

6.60.1 Wuri Da Lokacin Wasa

Kasancewar wasan na dandali ne, an fi gudanar da shi da dare, musamman lokacin farin wata.

5.60.2 Yadda Ake Wasa

Yara sukan tsaya bisa tsarin da’ira. Daga nan za su riƙa fitowa ɗaya bayan ɗaya suna ba da waƙa. Yayin da yarinya ke ba da waƙa, saura za su riƙa amsawa tare da tafi. Ga yadda waƙar take:

Bayarwa: Allah ba ni ba ni,

Amshi: Kaɗa.

 

Bayarwa: Allah ba ni kaɗa,

Amshi: Kaɗa.

 

Bayarwa: Na yi zare na kaina,

Amshi: Kaɗa.

 

Bayarwa: Na yanke zugage,

Amshi: Kaɗa.

 

Bayarwa: Na yi zane na kaina,

Amshi: Kaɗa.

 

Bayarwa: Na kai wa masoyi.

Amshi: Kaɗa.

6.60.3 Tsokaci

Wannan wasa ne da ke samar da nishaɗi ga yara. Sannan waƙar wasan na ɗauke da hoton ɗaya daga cikin al’adun Hausawa na samar da tufafi daga auduga. Sai dai za a iya hasashen cewa, ba kaɗen haƙiƙa ake nufi ba. A maimakon haka, mai waƙar na nufin Allah Ya ba ta arziki domin ta yi abin kanta. Wato ta dena dogara ga wasu.

WASANNI A ƘASAR HAUSA

Post a Comment

0 Comments