Sama Indo

    6.70 Sama Indo

    Wannan wasan yara mata ne da ke tafiya da waƙa. Kimanin yara goma zuwa sama da haka ke gudanar da shi. Ba ya buƙatar kayan aiki yayin gudanarwa.

    6.70.1 Wuri Da Lokacin Wasa

    Wannan wasa na dandali ne. Saboda haka an fi gudanar da shi da dare, musamman lokacin farin wata.

    6.70.2 Yadda Ake Wasa

    Yara sukan tsaya bisa tsarin da’ira. Daga nan yara za su fara shiga tsakiyar da’irar ɗaya bayan ɗaya. Wato dai idan ɗaya ta shiga ta gama, sai wata daban ma ta shiga. Yayin da yarinyar ke ciki, za a riƙa waƙa tare da tafi. Ita kuwa za ta riƙa wajijiya(hajijiya) da ƙarfi. Wani lokaci har jiri kan ɗauki wasunsu su faɗi, ko kuma abokan wasansu su riƙe su. Waƙar kuwa da ake yi ita ce:

    Sama Indo mai wa ya Rasulu,

    Mai wa Allah ya sauwaƙe,

    Ya yi ma amanar Indo Baturiya.

     

    Zaki ya yi karo da kai daji,

    Ya yi mai amanar Indo Baturiya.

    Ɓauna ta yi karo da kai daji,

    Ya yi mai amanar Indo Baturiya.

     

    Giwa tai karo da kai daji,

    Ya yi mai amanar Indo Baturiya.

     

    Kura tai karo da kai daji,

    Ya yi mai Indo Baturiya.

     

    Bari in gai da ‘yan maza daji,

    Ya yi mai Indo Baturiya.

    6.70.3 Tsokaci

    Wannan wasan motsa jini ne ga yara. Waƙar wasan tana daɗa zuga su domin ci gaba da hajijiya iyaka ƙarfinsu. Waƙar tana ɗauke da kirari ga masoya.

    WASANNI A ƘASAR HAUSA

    Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.