Cillo-Cillo

    Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.

    6.75 Cillo-Cillo

    Wannan ma wasan yara mata ne. Misalin yara shida zuwa sama ne suke gudanar da wannan wasa. Yana cikin rukunin wasannin mata da ke tafiya da waƙa. Sannan akan bukaci kayan aiki yayin gudanar da shi.Wannan wasa ne na dandali, saboda haka an fi gudanar da shi da dare. Sai dai a yau, yara da dama na gudanar da wannan wasa a makarantu.

    6.75.1 Kayan Aiki

    Ɗankwali/kallabi ko zane ko wani tsumma mai ƙarfi da ɗan tsawo

    6.75.2 Yadda Ake Wasa

    Akan naɗa ɗankwali guda ɗaya ko biyu a yi kewaye da su tamkar gammo. Daga nan kowace mai wasa za ta ɗaura ɗankwalinta jikin wannan gammo ta kuma riƙe ƙarshen. Wato dai za su kasance sun yi da’ira. Ɗaya daga cikinsu za ta zo ta hau bisa wannan gammo. Su kuwa da ke rirriƙe da ƙarshen kwalayen za su riƙa cilla ta sama (amma ba sosai ba), sai kuma ta dawo kan wannan gammo. Za kuma su riƙa yi suna waƙa kamar haka:

    Cillo-collo cilloriya,

    Cillo‘yattsamiya,

    Faɗo ki dagargaje,

    Tun ba a watan aurenki ba,

    Casa ɗaya,

    Casa biyu,

    Casa uku,

    Casa huɗu …

    Haka za a riƙa ƙirgawa har zuwa adadin da aka ƙiyasce. Da zarar an kammala, sai ta sauka wata daban kuma ta hau.

    6.75.3 Tsokaci

    Wannan wasa hanya ce ta motsa jiki ga yara. Sannan yana samar musu nishaɗi da annashuwa. Waƙar na ɗauke da raha da ban dariya. A rasa ranar da za a mata addu’ar faɗuwa da jin ciwo sai ranar aurenta?

    WASANNI A ƘASAR HAUSA

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.