Lokos

    6.76 Lokos

    Wannan ma wasa ne na yara mata. Kimanin adadin yara uku zuwa sama ne suke gudanar da wannan wasa. Wannan wasan dandali ne, saboda haka an fi gudanar da shi da dare, musamman lokacin farin wata. Yana tafiya da waÆ™a, amma ba ya buÆ™atar wani kayan aiki yayin gudanar da shi.

    6.76.1 Yadda Ake Wasa

    Yara biyu sukan riÆ™e hannuwa. ÆŠaya kuwa za ta je nesa kaÉ—an da su. Sai kuma ta dawo wurin da suke. Daga nan za ta ce:

    “Locos.”

    Yara biyu da riÆ™e da hannuwa kuwa za su ce:

    “Kasuwar mata.”

    Sai wannan yarinya ta tambaya:

    “Nawa ne?”

    Sai su ce:

    “Ishirin da biyar.”

    Sai kuma ta ce:

    “Sha biyar.”

    Sai su kuwa su ce:

    “Ban ga dama ba.”

    Daga nan yarinyar za ta juya kamar za ta tafi, sannan ta ce:

    “To na tafi.”

    Yaran kuwa za su ce:

    “Haba bebi bebi zo ki hau.”

    Da zarar sun faÉ—i haka, yarinyar za ta zo da gudu ta haye bisa hannuwansu. Su kuwa za su riÆ™a lila ta suna Æ™irge:

    ÆŠaya,

    Biyu,

    Uku … 

    Haka za a yi ta Æ™irgawa har zuwa adadin da suka iyakance. Daga nan sai ta sauÆ™a wata kuma ta karÉ“a.

    6.76.2 Tsokaci

    Wannan wasa hanya ce ta motsa jiki ga yara. Sannan yana samar wa yara nishaÉ—i.

    WASANNI A ƘASAR HAUSA

    Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.