Dura-Dura

    6.79 Ɗura-Ɗura 

    Wannan wasan yara mata ne da ake gudanarwa tsakanin mutane biyu ko sama da haka. Wasa ne na nuna ƙwarewa da bajintar amfani da hannu. Wasan yana buƙatar kayan aiki yayin gudanar da shi. Sannan yana tafiya da lissafi da ake rerawa a sigar waƙa.

    6.79.1 Wuri Da Lokacin Wasa

    i. Akan gudanar da wannan wasa a dandali ko a gidajen buki kamar bukin aure ko na haihuwa, ko kuma wani wuri da ake samun taron yara mata.

    ii. An fi gudanar da wannan wasa da hantsi ko da yamma kasancewar akan bukaci wadataccen haske yayin da ake gudanar da wasan.

    6.79.2 Kayan Aiki

    Ƙananan duwatsu ko ɗanyar kanya ko wani abu mai kama da wannan

    6.79.3 Yadda Ake Wasa

    Masu wasa za su nemo ƙananan duwatsu ko ɗanyar kanya ko makamancin wannan, kowa guda bibbiyu. Daga nan wadda za ta fara wasa za ta riƙe dutse ɗaya a hannun dama ɗaya kuwa a hagu – idan wasan ɗan hannu biyu ne. Sai ta riƙa cilla su sama cikin ƙwarewa tare da canza musu hannu. Wato sai ta riƙe na hannun dama da hannun hagu, na hannun hagu kuwa ta cafe shi da hannun dama. Da zarar ta faɗi, sai abokiyar wasanta ta karɓa.

    Idan wasan ɗan hannu ɗaya ne kuwa, da hannu guda mai wasa za ta riƙa cilla duwatsun. Amma wani abin gwaninta shi ne, kafin dutse ɗaya ya sauko, ta cilla wanda ke hannunta. Haka shi ma kafin ya dawo, ta cafe ɗayanta sannan ta sake cilla shi. Wasu sukan yi ɗan dutse uku, musamman idan wasan ɗan hannu biyu ne.

    Yayin da mai wasa ke yi, za ta riƙa ƙirge cikin waƙa. Salon waƙar ta danganta da idan ɗurawa take yi ko fanshewa. Za ta iya kasancewa, wadda ta fara ɗurawa a fanshe ɗurin da ta yi, har a ɗura mata wasu da dama. Waƙar ɗurawa ita ce kamar haka:

    Ɗura-ɗura ɗaya,

    Ɗura-ɗura biyu,

    Ɗura-ɗura uku …

    Ɗura-ɗura goma,

    Goma ya ban ɗaya,

    Goma ya ban biyu,

    Goma ya ban uku …

     

    Ishina,

    Ishi ya ban ɗaya,

    Ishi ya ban biyu,

    Ishi ya ban uku …

     

    Talana,

    Tala ya ban ɗaya,

    Tala ya ban biyu,

    Tala ya ban uku …

    Wadda take fanshewa kuwa, za ta riƙa waƙa kamar haka:

    Fanshe-fanshe ɗaya,

    Fanshe-fanshe biyu,

    Fanshe-fanshe uku …

    Fanshe-fanshe goma,

    Goma ya ban ɗaya,

    Goma ya ban biyu,

    Goma ya ban uku …

     

    Ishina,

    Ishi ya ban ɗaya,

    Ishi ya ban biyu,

    Ishi ya ban uku …

     

    Talana,

    Tala ya ban ɗaya,

    Tala ya ban biyu,

    Tala ya ban uku …

    Wani lokaci akan dakata da wasa ba a ce sai haɗuwa tagaba za a ci gaba. Za a iya tashi da wasa yayin da aka ɗura wa wata ɗaruruwa ko ma sama da dubu. A nan za ta ƙulla aniyar cewa, idan aka sake haɗuwa za ta fanshe har ma ta ɗura.

    6.79.4 Tsokaci

    Wannan wasa na samar da nishaɗi ga yara. Sannan hanya ce ta ƙwarewa ga amfani ko sarrafa hannu.

    WASANNI A ƘASAR HAUSA

    Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.