Mamin Jatau

    6.80 Mamin Jatau 

    Wannan wasa ne da ake aiwatarwa tsakanin mutane biyu zuwa sama da haka. Mutane biyu ne suke gudanar da wasan a lokaci guda. Saboda haka, idan ya kasance yara da yawa ne suka taru domin wasan, za su riÆ™a yi ta bibbiyu. Yayin da É—aya ta faÉ—i, sai wata ta karÉ“e ta.

    6.80.1 Wuri Da LokacinWasa

    i. Wannan wasa ba shi da takamaiman lokacin da ake gudanar da shi. Akan yi wasan a dandali ko makarantun boko ko kuma wuraren da yara ke taruwa.

    ii. Babu wani takamaiman lokacin da ake gudanar da wannan wasa. Akan yi shi da hantsi ko da yamma ko ma da dare.

    6.80.2 Yadda Ake Wasa

    Yara sukan tsaya su fuskanci juna. Daga nan za su riÆ™a tafa hannuwansu cikin salo-salo. Yayin da suka tafa da juna, sai kuma su yi tafi (wato yarinya za ta yi tafi sannan ta kai hannu su tafa da ‘yaruwarta). Salon tafin da yara ke yi sun bambanta daga wuri zuwa wuri. Yara kan yi waÆ™a yayin da suke gudanar da wannan wasa. Ga waÆ™ar kamar haka:

    Mamin jatau mi,

    Tashin wulbairo,

    Bairo-bairo mi,

    Ai liki-liki laila,

    Wulbari laila,

    Tashina laila,

    Tashin makaranta laila.

     

    Is ma e gud e gud e gud ala conturol,

    Mamanta‘yar banza,

    Ta sace min nera.

     

    Babata ta ce,

    In ta je mak-mak-mak,

    In ta je Makka,

    Za ta sayo yoyo,

    Za ta sayo min,

    ÆŠankwalin dis-dis-dis,

    ÆŠankwalin disko.

    6.80.3 Tsokaci

    Wannan wasa hanya ce ta motsa jiki ga yara, sannan yana samar da nishaÉ—i gare su. Baya ga haka, wasan na koyar da Æ™warewa wurin amfani da hannu ga yara.

    WASANNI A ƘASAR HAUSA

    Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.