Soyayya Iri-Iri Ce

    6.81 Soyayya Iri-Iri  Ce

    Wannan ma wasan yara mata ne da ke tafiya da waƙa. Yana cikin rukunin wasannin dandali na gaɗa. Saboda haka an fi gudanar da shi da dare, musamman lokacin farin wata. Yawanci akan samu taron yara da yawa yayin gudanar da wannan wasa. Adadinsu na iya kaiwa goma sha biyar ko ma sama da haka. Sannan wasan ba ya buƙatar wani kayan aiki yayin da ake gudanar da shi.

    6.81.1 Yadda Ake Wasa

    Yara za su tsaya a bisa tsarin da’ira. Daga nan za su riƙa shiga tsakiyar da’irar ɗaya bayan ɗaya suna rera waƙa. Sauran yara kuwa za su riƙa amshi tare da tafi da kuma rawa. Ga yadda waƙar take:

    Bayarwa: Soyayya ba ƙiyayya ba,

    Amshi: Soyyayya ba ƙiyayya ba.

     

    Bayarwa: Soyayya iri-iri ce,

    Amshi: Soyyayya ba ƙiyayya ba.

     

    Bayarwa: Akwai ta kuɗi akwai ta zobe,

    Amshi: Soyyayya ba ƙiyayya ba.

     

    Bayarwa: Akwai ta ganin idon masoyi,

    Amshi: Soyyayya ba ƙiyayya ba.

     

    Bayarwa: Wata na a ƙarƙashin zuciya,

    Amshi: Soyyayya ba ƙiyayya ba.

     

    Bayarwa: Tun ba a yo mu duniya ba,

    Amshi: Soyyayya ba ƙiyayya ba.

     

    Bayarwa: Ke tashi raka ni gun masoyi,

    Amshi: Soyyayya ba ƙiyayya ba.

     

    Bayarwa: Tashi mu je wurin masoyi,

    Amshi: Soyyayya ba ƙiyayya ba.

     

    Bayarwa: Masoyi ne ke kiran mu,

    Amshi: Soyyayya ba ƙiyayya ba.

    6.81.2 Tsokaci

    Wannan wasa yana samar da nishaɗi ga yara. Sannan waƙar wasan na ɗauke da wani saƙo game da soyayya. Kamar yadda waƙar ke bayyanawa, soyayya akwai ta ƙarya da kuma ta gaskiya. Wato akwai so da ake yi saboda kwaɗayi ko ganin ido kawai.

    WASANNI A ƘASAR HAUSA

    Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.