Goye-Goye

    6.87 Goye-Goye 

    Wannan ma wasan yara mata ne da suka fi gudanarwa a dandali. Yara biyu ne suke wasan goye-goye a tsakaninsu. Yayin da aka samu taron yara da yawa, kowacce za ta kama abokiyar goye-goyenta. Akan yi wannan zaÉ“i ne ta la’akari da girman jiki da kuma Æ™arfi. Wato dai kowa takan kama daidai da ita, Æ™warya ta bi Æ™warya. Wannan wasa ne na dandali, saboda haka an fi gudanar da shi da dare, lokacin farin wata.

    6.87.1 Yadda Ake Wasa

    Yara sukan Æ™iyasce wani wuri mai É—an tazara a filin wasa. Wannan wuri shi ne za a riÆ™a zuwa. Daga nan É—aya za ta goyi É—aya ta nufi wurin da ita. Wasan na kasancewa idan yarinya ta goyi abokiyar wasanta zuwa can, to abokiyar ce za ta goyo ta ta dawo da ita. Wani lokaci kuma ana ‘yar zuwa da dawowa. Wato za a goyi yarinya a kai ta a dawo da ita. Daga nan ita ma sai ta rama wa abokiyarta.

    6.87.2 Tsokaci

    Wannan wasa hanya ce ta motsa jiki ga yara. Sannan yana samar da nishaÉ—i gare su.

    WASANNI A ƘASAR HAUSA

    Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.