Kifi-Kifi

    6.90 Kifi-Kifi 

    Wannan ma wasan dandali ne na yara mata. Kimanin yara goma zuwa sama ne suke gudanar da wannan wasa. Wasan yana da sigar kwalba-kwalba dire ta fuskar cilli da direwa. Amma sun bambanta ta É“angarori da dama. Kasancewar wasan  na dandali, an fi gudanar da shi da dare, musamman lokacin farin wata. Ba a buÆ™atar wani kayan aiki yayin gudanar da shi. Sannan yana tafiya da waÆ™a.

    6.90.1 Yadda Ake Wasa

    Yara za su rabu kashi biyu. Za su kasance suna fuskantar juna. Amma za su bar tazara mai É—an faÉ—i a tsakaninsu. Daga nan yara biyu za su fito tsakiya, waÉ—anda kuma su ne masu direwa. Daga nan za a fara waÆ™a tare da tafi. WaÉ—annan yara biyu na tsakiyar fili za su riÆ™a faÉ—awa hannun waÉ—anda ke tsattsaye. ÆŠaya za ta faÉ—a wa É“angare É—aya, É—ayar kuma za ta faÉ—a É—aya É“angaren. WaÉ—anda ke tsayen kuwa za su cillosu a tare. Daga nan sai su canza wurin faÉ—awa. Wato wadda ta faÉ—a hannun dama da sai ta komo hannun hagu. Haka ma wadda ta faÉ—a hannun hagu za ta koma hannun dama. Za su riÆ™a yi suna waÆ™a kamar haka:

    Kifi-kifi-kifi,

    Kifin Malam Sale,

    Ga daÉ—i ga kwaÉ—ayi.

     

    Shi ma Malam Sale,

    Ga daÉ—i ga kwaÉ—ayi.

    Da zarar an kamala wannan waÆ™a, masu direwa za su koma cikin sauran ‘yanwasa. Wasu daban kuma za su fito tsakiya. 

    6.90.2 Tsokaci

    Wannan wasa yana sanya nishaÉ—i ga yara. Sannan hanya ce ta motsa jiki gare su.

    WASANNI A ƘASAR HAUSA

    Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.