Rabi Da Audu

    6.95 Rabi  Da Audu 

    Wannan wasa na ya faɗo ne cikin rukunin wasannin tashe na yara mata. Yana tafiya da waƙa. Sannan ana buƙatar kayan aiki yayin gudanar da shi. Kimanin yara biyar ne zuwa sama da haka suke gudanar da wannan wasa. A cikinsu za a samu Rabi da Audu da kuma sauran ma su ba da waƙa. Akan gudanar da ita da hantsi ko da yamma ko da dare bayan an sha ruwa, a watan azumi.

    6.95.1 Kayan Aiki

    i. Kayan maza manya (babbar riga da hula da rawani da makamantansu)

    ii. Auduga (wanda ake sanyawa a matsayin gemu da saje)

    iii. Wani mai danƙo (domin maƙala gemu da sajen auduga)

    iv. Farar ƙasa ko goli ko wani abu mai kama da wannan (domin shafawa a matsayin furfura)

    6.95.2 Yadda Ake Wasa

    Yayin da yara suka taru domin wasa, za a samu ɗaya daga ciki ta yi shigar maza. Wannan ita ake kira Audu. Za ta sanya kayan maza dattawa, kamar su babbar riga da hula da rawani. Sannan za a mata sajen auduga. A ɗaya ɓangaren kuma, wata yarinyar da ban za ta yi shigar dattijuwa. Wato tsohuwa mai furfura. Shi ma wannan furfura akan shasshafa farin abu ne da zai sanya gashin ya kasance tamkar furfura.

    Daga nan za su wuce gaba, sauran yara kuwa na biye. Yayin da suke cikin gida domin tashe. Waɗannan yara biyu, Rabi da Audu za su riƙa tiƙar rawa, cikin takuirin na masu yawan shekaru. Sauran yara kuwa za su sanya waƙa, yayin da Rabi da Audu za su riƙa amsawa. Ga yadda waƙar take.

    Bayarwa: Masu gida ku fito ku yi kallo,

    Rabi da Audu suna cashewa.

     

    Rabi da Audu: Don ma ba mu hau titi ba,

    In muka hau titi ba wasa.

    Haka za su ci gaba da yi har sai an sallame su.

    6.95.3 Tsokaci

    Wannan wasa na samar da nishaɗi ƙwarai, musamman ga masu kallo. Ga masu wasa kuwa, hanya ce ta nishaɗi da kuma samun abin masarufi. An gina wannan wasa domin nishaɗantarwa da ban dariya. Sai Allah Ya san dalilin wannan rawa ta Rabi da Audu. Ko iskar funturu ce ta busa su?

    WASANNI A ƘASAR HAUSA

    Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.